'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Halaka Dan Kasuwa da Sace Manoma 4 a Borno

'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Halaka Dan Kasuwa da Sace Manoma 4 a Borno

  • Ƴan ta'addan Boko Haram sun kai farmaki a gonar wani ɗan kasuwa a ƙaramar hukumar Bama ta jiahr Borno
  • Miyagun ƴan ta'addan a yayin harin sun halaka ɗan kasuwan mai suna Alhaji Goni tare da sace mutum huɗu da ke masa aiki a gonarsa
  • Marigayin dai wanda ake yi wa aikin girbin wake ya rasa ransa ne bayan ya ƙi yarda ƴan ta'addan su yi garkuwa da shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Jihar Borno - Ƴan ta'addan Boko Haram sun harbe wani ɗan kasuwa a Maiduguri har lahira a ranar Lahadi, mai suna Alhaji Gana, a gonarsa da ke ƙaramar hukumar Bama a jihar Borno.

Lamarin ya faru ne a lokacin da ake girbin wake a gonarsa inda aka yi garkuwa da masu yi masa aiki mutum huɗu, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai kazamin hari a jihar Zamfara, sun yi awon gaba da mutum 5

'Yan ta'addan Boko Haram sun halaka dan kasuwa
'Yan ta'addan Boko Haram sun halaka dan kasuwa a gonarsa a Borno Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewar wata majiya daga iyalan mamacin, ƴan ta'addan sun yi awon gaba da mutum huɗun ne da ƙarfin tsiya, amma an harbe shi har lahira a lokacin da ya ƙi yarda a sace shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka halaka Alhaji Goni

Majiyar ta bayyana cewa:

"Sauran manoman da ke kusa da wurin da lamarin ya faru, tun daga nesa sun ce sun hango shi yana ta kokawa da ƴan ta'addan na wani ɗan lokaci kafin daga bisani maharan su rinjaye shi."
"Ƴan ta'addan sun farmaki gonar, inda suka zagaye ma'aikatan, sannan suka yi yunƙurin yin garkuwa da su. An harbe Alhaji Gana bayan ya bijirewa maharan. Maharan sun yi garkuwa da wasu mutum huɗu, inda suka bar gawar Alhaji Gana a cikin gonar."

Wani ɗan uwansa mai suna Abdul Mohammed ya ce Alhaji Gana ya bar Maiduguri ne da safiyar Lahadi domin lura da yadda ake girbi a gonarsa ta Bama, inda ya rasa ransa a can.

Kara karanta wannan

Ya yi shahada: Wani matashin magidanci ya rasu a ƙoƙarin kare mutuncin matarsa a jihar Bauchi

"Ya shaida wa matarsa ​​cewa zai dawo da wani daga cikin waken da ake girbi a gonarsa. Bayan ƴan sa'o'i kaɗan, an kira su cewa ƴan ta'adda sun halaka shi." A cewarsa.

Ƴan ta'adda na yawan kai hare-hare kan manoma a jihar Borno, musamman a lokacin da ake tsakiyar girbin amfanin gona.

Mayakan Boko Haram Sun Halaka Limami

A wani labarin kuma, ƴan ta'addan Boko Haram sun halaka wani babban limami a ƙaramar hukumar Kaga ta jihar Borno.

Ƴan ta'addan sun farmaki gidan Imam Goni Muktar, babban limamin Kaga a cikin gidansa sannan suka halaka shi har lahira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng