Zan Kore Ku, Ba Zan Bari Shugabannin Hukumomi Su Jawo Tinubu Ya Tsige Ni ba – Minista

Zan Kore Ku, Ba Zan Bari Shugabannin Hukumomi Su Jawo Tinubu Ya Tsige Ni ba – Minista

  • Ministan harkokin jiragen sama ya yi barazanar tsige shugabannin ma’aikatarsa kafin ya rasa kujerarsa a gwamnati
  • Festus Keyamo ya tara wadanda su ke rike da mukamai a karkashinsa, ya fada masu wajibi ne su goya masa baya a aikinsu
  • Kafin wani ya yi sanadiyyar da gwamnatin Bola Tinubu za ta yi waje da Ministan, Keyamo ya ce shi zai fara ganin bayan shi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Ministan da ke kula da harkokin jiragen sama a Najeriya, Festus Keyamo, ya ja-kunnen shugabannin hukumomin da ke karkashinsa.

Ganin ya sa hannu a yarjejeniyar yin aiki, Daily Trust ta rahoto Festus Keyamo ya na cewa ya zama masa dole ya sauke nauyin da ke kan sa.

Kara karanta wannan

Fitaccen malamin addini ya bayyana mafita 1 tak ga matsalolin Najeriya

Festus Keyamo SAN ya nemi goyon bayan masu ruwa da tsaki domin ya tsira da aikinsa. Hakan na zuwa ne makonni bayan shiga ofis.

Minista
Ministan jirage a kasar waje Hoto: Festus Keyamo, SAN, CON, FCIArb (UK); @fkeyamo
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu zai kori Ministan da bai kokari

A wajen wani taro da aka shiryawa Ministoci da Mukarrabai, duk sun sa hannu cewa za su yi ayyukan da ake bukata, ko kuwa ayi waje da su.

Bayan nan ne Keyamo ya kira taron kwana guda da masu ruwa da tsaki a Legas, karon farko da ya zauna da su kenan bayan ya zama Minista.

Jawabin Ministan jirage, Festus Keyamo

"Mun yi taron bitan kwanaki uku da Mai girma shugaban kasa, duka Ministoci. A karshe, mun sa a hannu a yarjejeniyar yin aiki.

Na kuma sa hannu a ta wayarjejeniyar a jiya. Saboda haka idan ba ku so a tsige ni nan da ‘yan watanni, sai ku mara mani baya.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu da hatsarin jirgin sama ya rutsa da shi ya magantu, ya faɗi halin da yake ciki

- Festus Keyamo

Vanguard ta rahoto Ministan ya ce ba zai bari masu rike da hukumomi, cibiyoyi da ma’aikatun jiragen sama su yi sanadiyyar rasa mukaminsa ba.

"A bangaren nan, ko dai a fatattake ni ko kuwa a fatattake su. Saboda haka, tsere ne da za a ga wanda zai kubuta.
Abin da na fadawa duka shugabannin hukumomi na kenan, dole wani ya mutu, amma kafin in mutu, zan kashe ku."

-Festus Keyamo

Abacha ya saci kudin Najeriya?

Ana haka sai aka ji Uche Rochas ya na cewa Janar Sani Abacha bai saci kudin Najeriya daga baitul-mali ba, ya saida mai ne ta bayan fage.

‘Dan siyasar yake cewa bayan mutuwar Abacha ne kasashen waje su ka nemi satar kudin kasar, sai aka dawo ana gogawa marigayin kashi a jiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng