“Takun Kudi”: Bidiyon Diyar Dangote Tana Rawan Kasaita Ya Dauka Hankali

“Takun Kudi”: Bidiyon Diyar Dangote Tana Rawan Kasaita Ya Dauka Hankali

  • Wani bidiyon diyar mai kudin Afrika, Aliko Dangote, tana rawa da more tayuwa a wajen wani taro ya yadu a dandalin TikTok
  • Kyakkyawar matashiyar, wacce ta kasance darakta a kamfanin mahaifinta, ta ware dan lokaci domin jin dadin rayuwarta
  • Ta kasance cikin farin ciki da walwala yayin da take nuna ita gwana ce a bangaren rawa, tana mai taku daidai cike da nutsuwa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani bidiyo mai jan hankali na diyar attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote, tana taka rawa a wajen wani taro ya dauki hankalin mutane a TikTok.

Kyakkyawar matashiyar, wacce ta kasance mamba a kwamitin katafaren kamfanin mahaifinta na biliyoyi, ta warewa kanta lokaci domin more rayuwarta.

Kara karanta wannan

“Kasuwa ta yi kyau”: Mabaraciya ta siya soyayyar kaza, ta darje ta zabi wanda take so

Dangote tare da diyarsa
“Takun Kudi”: Bidiyon Diyar Dangote Tana Rawan Kasaita Ya Dauka Hankali Hoto: @halimadangoteoffi
Asali: TikTok

Alamunta sun nuna tana cikin jin dadi da annashuwa yayin da take taku daidai cike da nutsuwa a lokacin da sauti ke tashi a dakin taron da ta halarta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon ya dauka hankali sosai sannan ya tara martani daga masu amfani da TikTok, wadanda suka yaba mata saboda yanayin shigarta ta mutunci da kasancewa mai faran-faran duk da tarin arziki da shaharar mahaifinta a duniya.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan bidiyon diyar Dangote tana rawa

Madam tee ta yi martani:

Dole kiyi rawa my sister, ku kude Nigeria, gaisuwa daga wannan bangaren."

Samirahammanjodau ta ce:

"Salam hajiya don Allah ina bukatar aiki na karanci bangaren hada-hadar kudi."

Aisha falke ta rubuta:

"Gaskiya na so wadannan bidiyoyin!! Muna samun ganinki."

Useró838741704627 ya yi martani:

"Ba ki da kowace matsala saboda mahaifinki na da kudi ki ji dadinki."

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da walkiya ta kashe dalibai suna tsaka da buga kwalla a Anambra

ShamsuddeenMijinyawa:

"Baki iyya rawa ba ee."

Abbadecoration:

"Kariyar Allah yar'uwara. Ki ji dadin rayuwa Anti."

Dpo73636:

"Hajiya ta iya rawa sosai."

RU20097:

"Takun kudi."

User4001288210738:

"Yo ba ruwanki da tsadar sugar bare ta flour."

Jaruma Rashida za ta amarce

A wani labarin, mun ji cewa fitacciyar jaruma Rashida Adamu Abdullahi wacce aka fi sani da Rashida Mai Sa'a za ta amarce.

Za a daura auren Rashida da angonta mai suna Alhaji Aliyu Adamu, Sardaunan matasan Gwoza a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng