Shugaba Tinubu Zai Shilla Kasar Saudiyya a Mako Mai Zuwa, an Fadi Abin da Zai Yi a Tafiyar

Shugaba Tinubu Zai Shilla Kasar Saudiyya a Mako Mai Zuwa, an Fadi Abin da Zai Yi a Tafiyar

  • Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zai kai ziyara kasar Saudiyya don halartar taron kasashen Labarawa da na nahiyar Afrika
  • An ce taron zai taimaki Najeriya da sauran kasashen Afrika ta hanyoyi da dama da suka shafi tattalin arziki da sufuri
  • Shugabannin Najeriya na yawan halartar taro a kasashen waje, hakan na jawo a kashe makudan kudade masu yawan gaske

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

FCT, Abuja - Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, ya bayyana cewa, Shugaba Tinubu zai kai ziyara kasar Saudiyya domin halartar taro don jawo hankulan ‘yan kasuwa da masu zuba hannun jari zuwa Najeriya.

Wannan na zuwa ne a lokacin da hadimin na Tinubu ke zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe mutum 5, sun jikkata 4 yayin da suka kai farmaki a jihar Sokoto

Tinubu zai kai ziyara Saudiyya
Tinubu zai tafi kasar Saudiyya ziyara a taron kasashen Larabawa | Hoto: OfficialABAT
Asali: Twitter

An bayyana cewa, taron zai hada shugabannin kasashe daban-daban na Larabawa, inda za a tattauna kan bautuwa da dama da suka shafi alakar juna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makasudin zuwan Tinubu Saudiyya

Ngelale ya bayyana cewa, makasudin halartar Tinubu taron shi ne kara habaka alakar kasuwanci da zuba hannun jari tsakanin Masarautar Saudiyya da nahiyar Afirka.

Tinubu zai halarci taron ne da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba a matsayinsa na shugaban kungiyar gamayyar ci gaban tattalin arzikin kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS.

Halartarsa, in ji Ngelale, zai kara dankon zumunci tsakanin kungiyar kasashen Larabawa da kungiyar Tarayyar Afirka, TheCable ta ruwaito.

Karin haske game da makomai taron

Ya kara da cewa:

"Wannan zai samar da hadin kai ta fuskar samar da ababen more rayuwa, gudanarwa da kuma kafa sabuwar hanyar jirgin kasa mai sauri wacce za ta hada kasashen Larabawa daga Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka, da sauran kasashen nahiyar."

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta raba gardama, ta yanke hukunci kan nasarar tsohon gwamnan Gombe

Shugabannin Najeriya sun iya fita kasashen waje halartar taruka, amma shin hakan na da tasiri ga ci gaba ko kuma kashe kudin kasa ne kawai kwalliya bata biya kudin sabulu ba?

Tinubu ya kashe miliyoyi a kama otal a Amurka

A wani labarin, kudin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta kashe a wajen halartar taron majalisar dinkin duniya kwanaki ya jawo surutu a gida.

Binciken jaridar FIJ ya nuna gwamnatin tarayya ta batar da $507,384 domin tawagar shugaban kasa ta kama dakuna kurum a dankareren otel.

Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya na cikin wadanda su ka je babban taron da majalisar dinkin duniya ta shirya a New York a Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.