An Maka Shugaba Tinubu Kara a Kotu Kan Bacewar $15bn da N200bn
- Ƙungiyar SERAP ta maka shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ƙara kan ɓacewar kuɗaɗen shiga na man fetur da kuɗin gyaran matatun man fetur
- Kuɗaɗen dai an yi zargin sun yi ɓatan dabo ne a tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021 a wani rahoto da NEITI ta fitar
- SERAP na neman kotu da ta tilasta Shugaba Tinubu ya sanya a gudanar da bincike kan ɓacewar kuɗaɗen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi
Jihar Legas - Ƙungiyar SERAP ta kai ƙarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan gazawar gwamnatinsa wajen gudanar da bincike kan zargin ɓacewar kuɗaɗen shiga na man fetur $15bn da N200bn da aka ware domin gyara matatun man fetur.
Kuɗaden dai ana zargin sun yi ɓatan dabo ne a tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021.
Waɗannan zarge-zargen dai na ƙunshe ne a cikin rahoton NEITI na shekarar 2021.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
SERAP ta shigar da ƙarar ne mai lamba FHC/L/CS/2334/2023 a ranar Juma'a, 3 ga watan Nuwamba, a babbar kotun tarayya da ke Legas.
Waɗanne buƙatu SERAP ke nema a gaban kotun?
SERAP na neman kotun ta tilasta shugaban ƙasa ya yi bincike kan zargin ɓacewar $15bn na kuɗaɗen shiga na maɓ fetur da N200bn da aka ware domin gyaran matatun man fetur na Najeriya.
SERAP na neman kotun ta tilasta Shugaba Tinubu da ya umarci hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da suka dace su binciki zargin almundahana da suka haɗa da kamfanin NNPC da hukumomin NPDC da SOE.
SERAP tana kuma neman kotun ta tilastawa Shugaba Tinubu yin amfani da duk kuɗaɗen da aka ƙwato na cin hanci da rashawa domin inganta rayuwar ƴan Najeriya.
Lauyoyin SERAP Kolawole Oluwadare, Andrew Nwankwo, da Ms Valentina Adegoke ne suka shigar da ƙarar a madadin SERAP.
SERAP Ta Shigar da Gwamnoni Ƙara
A wani labarin kuma, ƙungiyar SERAP ta maka gwamnonin Najeriya 36 ƙara a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Legas.
Ƙungiyar ta maka gwamnonin ƙara ne kan gazawarsu na bayar da gamsassun bayanai kan N72bn na tallafin da gwamnatin tarayya ta ba su domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Asali: Legit.ng