Ba Shi da Son Duniya, Bagudu Ya Fadi Inda Tinubu Ya Ke Kwana Kafin Zama Shugaban Kasa
- Yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan siyan jirgin ruwan alfarma na Tinubu, Minista Bagudu ya kare shugaban
- Ministan Kasafi da Tsare-tsare ya ce Shugaba Tinubu mutum ne mai kan-kan da kai wanda bai damu da abin duniya ba
- Bagudu ya bayyana haka ne a jiya Juma'a 3 ga watan Nuwamba yayin taron kara wa juna sani na ministoci a Abuja
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Ministan Kasafi da Tsare-tsare a najeriya, Atiku Bagudu ya bayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin mutum mai kan-kan da kai.
Bagudu ya bayyana haka ne a jiya Juma'a 3 ga watan Nuwamba a Abuja yayin taron kara wa juna sani na ministoci na kwanaki uku.
Mene Bagudu ke cewa kan Tinubu?
Ministan na magana yayin kare shugaban kan cece-kuce da ake yi na siyan jirgin ruwan alfarma da ake zargin shugaban da yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce wannan jirgin ruwan da ake magana ba an siyo shi ba ne don amfanin shugaban kasar, cewar Daily Trust.
Ya ce:
"Wannan rashin fahimta da aka yi na jirgin sojin ruwan ya jawo kace-nace a kasar.
"Amma idan har a kasafin tiriliyan 2.2, kaso 95 ba wani matsala, ina tunanin ya kamata a yaba wa Shugaba Tinubu a kan haka."
Wane yabo Bagudu ya yi wa Tinubu?
Ya kara da cewa shugaban ba shi da wata bukata ta kayatarwa na jrigin ruwa, abin da ya cimma a rayuwarsa ya ishe shi, cewar Trust Radio.
Ya kara da cewa:
"Kafin ya zama shugaban kasa, ya na kwana ne a gida mai dakuna uku kacal a Abuja, ya na rayuwa cikin kan-kan da kai ba tare da son duniya ba."
Tinubu ya yi martani kan zargin siyan jirgin ruwa
A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya yi martani kan cece-kucen da ake yi cewa ya siya jirgin ruwan alfarma na makudan kudade.
Shugaban ya ce ba shi da abin da zai yi da wannan jirgin inda ya ce tsohuwar gwamnatin Buhari ce ta siye shi.
Asali: Legit.ng