'Yan Bindiga Sun Sace Matan Shugaban Karamar Hukuma a Jigawa

'Yan Bindiga Sun Sace Matan Shugaban Karamar Hukuma a Jigawa

  • An shiga cikin tashin hankali bayan ma su garkuwa sun sace matan shugaban karamar hukuma a jihar Jigawa
  • Shugaban karamar hukumar Kiyawa, Nasiru Ahmed shi ya tabbatar da haka ga BBC Hausa inda ya ce maharan sun sace matansa biyu
  • Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Lawan Adamu Shiisu ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce su na kokarin ceto su

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Jigawa – ‘Yan bindiga sun kai farmaki karamar hukumar Kiyawa a jihar Jigawa tare da sace matan shugaban karamar hukumar.

Shugaba karamar hukumar, Nasiru Ahmed ya bayyana wa BBC Hausa cewa ‘yan bindigan sun farmaki gidan nasa ne a daren jiya Juma’a 3 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

FG ta yi karin bayani, ta fara bincike yayin da jirgin sama dauke da ministan Tinubu ya yi hatsari

'Yan bindiga sun sace matan shugaban karamar hukuma a Jigawa
Mahara sun sake kai hari a jihar Jigawa. Hoto: Umar Namadi.
Asali: Facebook

Su waye maharan su ka sace a Jigawa?

Nasiru ya ce maharan sun kora mutane da dama kafin shiga gidan nasa da kuma sace iyalan nasa, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Maharan sun yi harbe-harbe kafin shiga ciki, daga nan kuma su ka dauki matana guda biyu kuma har yanzu su na tare da su.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Adamu Shiisu ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Asabar 4 ga watan Nuwamba.

Wane martani ‘yan sanda su ka yi a Jigawa?

Adamu Shiisu ya ce sun samu rahoton faruwar lamarin inda su ka yi gaggawar tura jami’ansu zuwa inda lamarin ya faru.

Amma ya ce kafin zuwan jami’an nasu, maharan sun riga sun yi garkuwa da matan shugaban karamar hukumar.

Ya ce rundunar su ta tura jami’ai ta ko wane lungu a karamar hukumar don ceto wadanda aka sacen.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe mutum 5, sun jikkata 4 yayin da suka kai farmaki a jihar Sokoto

Ya kara da cewa rundunarsu na bukatar gudunmawar al’umma da bayani da ke da alaka da garkuwar don ceto matan auren, cewar Premium Times.

Sojoji sun bankado masana’antar kera makamai a Plateau

A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar gano wani katafaren kamfanin kera makamai a jihar Plateau.

Rundunar ta sanar da cewa ta gano msana’antar ce a yankin Vom da ke karamar hukumar Jos ta Kudu da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.