Wasu Matasa 2 Sun Jefa Kansu a Babbar Matsala Yayin da Suka Sace Motar Simintin Ɗangote
- Wasu matasa biyu sun jefa kansu cikin matsala yayin da suka sace motar kamfanin simintin Ɗangote a jihar Ogun
- Jami'an yan sanda sun bi diddigi sun kama su bayan direba ya kai rahoton abin da ya faru caji ofis
- Kakakin ƴan sandan jihar Ogun ta bayyana cewa tuni waɗanda ake zargin suka amsa laifinsu kuma an fara ɗaukar matakan doka
Ahmad Yusuf, gogaggen edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum.
Jihar Ogun - Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun cafke wasu mutane biyu da laifin satar wata babbar mota mallakar masana’antar siminti ta Dangote da ke Ibese.
Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan jihar, Omolola Odutola, ita ce ta bayyana haka ga manema labarai a Abeokuta, babban birnin Ogun.
Ta ambaci sunayen waɗanda aka kama da zargin satar motar kamfanin simintin, sun haɗa da, Lawal da Mohammed Ndatotu, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Odutola ta ce direban babbar motar da ke aiki a sashin sufuri na simintin Dangote a Ibese ne ya kai rahoton cewa an sace motar da yake ja mai lamba KPF 237 XA.
Kakakin ƴan sandan ta ce direban ya gaya wa ƴan sanda cewa babbar motar ta ɓata ne yayin da ya tafi ya bar yaran mota biyu, Mohammed Lawal da Isma'il a ciki.
A kalamanta, Odutola ta ce:
"Bayan ya dawo wurin ajiye motoci a ranar 29 ga Oktoba, 2023, direban ya faminci cewa an ɗauke motarsa zuwa wani wuri da ba a sani ba, kuma yaran biyu sun gudu."
"Daga baya babban jami’in ‘yan sanda na caji ofis ɗin Ogbere (DPO) ya bi sawun Lawal da Mohammed Ndatotu ya kuma damƙe su a Ogbere.”
Wane mataki aka ɗauka a kansu?
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan ta ƙara da bayanin cewa tuni waɗan da ake zargin suka masa laifinsu na sace motar daga wurin ajiye motoci.
Ta ce jami'an ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike kan lamarin tare da daukar matakan da suka dace kamar yadda doka ta tanada, Daily Post ta ruwaito.
Zamfara ta samu kayan agajin gaggawa
A wani rahoton kuma Gwamnan Zamfara ya karɓo kayan agajin gaggawa na al'ummar jihar Zamfara waɗan da lamarin yan bindiga ya shafa.
Dauda Lawal ya karɓi kayayyakin ne yayin da ya kai ziyara ga hukumar kula da ƴan gudun hijira da bakin haure ta ƙasa a Abuja.
Asali: Legit.ng