"Gwamnatin Tinubu Za Ta Tsamo Yan Najeriya Miliyan 50 Daga Kangin Talauci," Betta Edu

"Gwamnatin Tinubu Za Ta Tsamo Yan Najeriya Miliyan 50 Daga Kangin Talauci," Betta Edu

  • Gwamnatin Tinubu ta shirya tsamo 'yan Najeriya miliyan 50 daga kangin talauci, kamar yadda Ministar jin kai, Betta Edu ta bayyana
  • Betta Edu ta sanar da cewa yanzu haka gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin raba wa talakawa N25,000 na tsawon watanni uku, akalla iyalai miliyan 61 za su amfana
  • Gwamnatin tarayyar ta dauki matakin tantance wadanda za su ci gajiyar shirin ta hanyar duba NIN da BVN din su, don gudun tura wa mutanen bogi kudi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana wasu daga cikin matakan da ta dauka domin tsamo 'yan najeriya miliyan 50 daga kangin talauci, bisa umurnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Cin zarafi: Kungiyar NLC ta fadi ranar tsunduma yajin aiki, ta tura bukatu 6 ga gwamnati

Ministar jin kai da kawar da fatara, Betta Edu, ta bayyana hakan a ranar Alhamis, yayin wani taro na masu ruwa da tsaki na gwamnatin tarayyar da ya gudana a dakin taron fadar shugaban kasa, Abuja.

Shugaba Tinu da Betta Edu
Betta Edu ta bayyana cewa, Shugaba Tinubu na kokari wajen kawar da talauci a Nigeria Hoto: Betta Edu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A ranar Laraba ne shugaban kasa ya sanar da cewa ministocinsa za su sanya hannu kan wata yarjejeniyar aiki a karshen taron ministoci, hadiman shugaban kasa, sakatarorin din-din-din da kuma manyan jami'an gwamnati, taron da zai gudana na tsawon kwanaki uku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Minista Edu ta gana da 'yan jarida

Edu, yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a fadar shugaban kasa, ta ce yanzu haka ana kan bayar da tallafin N25,000 ga kowanne gidan talaka a Najeriya karkashin shirin 'conditional cash transfer' wanda zai gudana na tsawon watanni uku, inda kowanne gida zai samu jimillar N75,000, duk a cikin shirin kawar da talauci a kasar.

Kara karanta wannan

“Ni ba waliyyi bane, Najeriya ba ta da matsala”, In ji Peter Obi

Ministar ta kuma bayyyana cewa duk da shirin an kawo shi ne don rage radadin talaucin da ake ciki sakamakon cire tallafin man fetur, sai dai zai taimaka wajen tsamo akalla gidaje miliyan 61 daga talauci.

Gwamnati na bin matakai don gudun tura kudi ga mutanen bogi - Edu

Edu, wacce ta ce an kaddamar da shirin ta yadda wadanda suka cancanci tallafin ne kawai zasu samu kudin, ta kuma ce gwamnati na nemo wadanda za su ci gajiyar shirin tare da tantance su ta hanyar NIN ko BVN din su, don tabbatar da cewa kowa ya samu kudin.

Ministar ta jaddada cewa gwamnati na bin abun a hankali ta yadda ba za ta zo tana biyan mutanen da a karshe ta gano na bogi ne, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Ko da aka tambaye ta game da batun tsamo 'yan Najeriya miliyan hamsin daga talauci, sai cewa ta yi:

Kara karanta wannan

Shugaban NLC ya magantu kan yadda aka lakada masa duka a jihar Imo

"Akwai shirye shirye da muka yi. Amma abu na farko da muka dukufa akan shi shine, shirin bayar da tallafin naira dubu ashirin da biyar ga kowanne gidan talaka a Najeriya, kuma shirin zai cigaba da gudana na tsawon watanni uku."

Shugaba Tinubu Zai Tsamo Yan Najeriya Miliyan 136 Daga Kangin Talauci

Ko a cikin watan Agusta, Ministar jin kai da kawar da fatara, Betta Edu ta bayyana shirin Shugaban Kasa, Bola Tinubu, na tsamo 'yan Najeriya kimanin miliyan 136 daga kangin talauci.

Dakta Bettta Edu ta bayyana cewa shugaban ƙasa ba zai lamurci ƙaruwar talakawa ba a ƙasar nan, lamarin da ya jima ya ci wa gwamnati tuwo a kwarya, Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.