Abin Bakin Ciki: An Sake Tsintar Gawar Wata Dalibar UNIPORT a Dakinta

Abin Bakin Ciki: An Sake Tsintar Gawar Wata Dalibar UNIPORT a Dakinta

  • Hankula sun sake tashi yayin da aka sake tsintar gawar wata dalibar jami'ar Fatakwal (UNIPORT)
  • Dalibar wacce aka bayyana sunan da Adaeze, an tsinci gawarta ne yashe a dakin kwananta da ke wajen makarantar
  • Shugabar sashen kula da dalibai na jami'ar, Chima Wokocha, ta ce an samu kwalbar maganin kwari kusa da gawar yarinyar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Fatakwal, Jihar Rivers - An tsinci gawar wata dalibar jami'ar Fatakwal (UNIPORT) wacce aka bayyana sunanta da adaeze a dakin kwananta da ke Aluu, karamar hukumar Ikwerre, jihar Rivers.

Kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa, dalibar na matakin karatu na biyu, kuma tana karantar ilimin akawu, an tsinci gawarta ne a ranar Juma'a, 3 ga watan Nuwamba a dakin kwanta da ke wajen makarantar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da walkiya ta kashe dalibai suna tsaka da buga kwalla a Anambra

An gano gawar dalibar UNIPORT a dakinta
An gano gawar dalibar UNIPORT a dakinta tare da wani kwalba a gefe. Hoto: UNIPORT 2023/2024 ADMISSION UPDATE
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar rahoton jaridar Legit, mutane sun balle kofar dakin nata, inda aka tsinci gawarta yashe kusa da wata kwalbar maganin kwari.

Shugabar sashen kula da dalibai ta UNIPORT, Chima Wokocha, wacce ta tabbatar da faruwar wannan lamari ta ce makwaftan Adaeze ne suka kai ta asibitin jami'ar.

Wokocha ta ce shuwagabannin jami'ar UNIPORT da hukumar 'yan sanda sun ziyarci dakin dalibar. Ta kuma ce an sanar da iyayen Adaeze faruwar lamarin.

"Jami'an hukumar 'yan sanda na tare da mu. Bincikenmu ya nuna cewa maganin kwari ta sha, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarta. An sami kwalbar maganin kwarin a kusa da gawarta."
"Iyayenta sun riga da sun ISO, ina tunanin yanzu haka suna shirye shiryen tafiya da gawarta."

An tsinci gawar wata dalibar UNIPORT a dakin saurayi

A wani rahoton Legit Hausa, an gano gawar wata daliba a mataki na uku a jami'ar Fatakwal (UNIPORT), Otuene Justina Nkang, a dakin saurayinta da ke babban birnin jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Yaudara ko don Allah? Yahaya Bello ya ware miliyan 497 don dalibai ana saura kwanaki 6 zabe a jihar

An ayyana batan Nkang kwanaki hudu da suka gabata bayan ta bar wajen aikinta, inda take koyon horo a wani asibiti mai zaman kansa a Fatakwal.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, wata majiya ta ce saurayin Nkang ya kashe ta sannan ya yanke nononta, ido da wasu sassan jiki.

An tsinci gawar dalibar Jami'ar FUOYE da ta bata

Wani labarin makamancin wannan daga Legit Hausa ya nuna yadda aka tsinci gawar wata dalibar jami'ar tarayya ta Oye Ekiti (FUOYE), Atanda Modupe Deborah.

An ayyana batan Atanda, dalibar sashin kula da jinya wacce ke a mataki na biyu bayan ta fita zuwa aji don yin karatu a daren ranar Litinin, 4 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.