Ya Yi Shahada: Wani Matashin Magidanci Ya Rasu a Ƙoƙarin Kare Mutuncin Matarsa a Bauchi

Ya Yi Shahada: Wani Matashin Magidanci Ya Rasu a Ƙoƙarin Kare Mutuncin Matarsa a Bauchi

  • A kokarin kare mutuncin matarsa, wani magidanci ɗan shekara 25, Ibrahim Ahmadu ya rasa rayuwarsa a jihar Bauchi
  • Hukumar ƴan sanda ta bayyana cewa wasu ƴan daba suka tare ma'auratan, suka nemi ya bar musu matarsa shi kuma ya ƙi yarda
  • A halin yanzu ana bincike kan lamarin kuma da zaran an kammala ƴan sanda zasu gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban Kotu

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum

Jihar Bauchi - Wani matashin magidanci ɗan shekara 25 a duniya, Ibrahim Ahmadu, ya rasa rayuwarsa yayin ƙokarin ceton matarsa, Amina Sani, daga sharrin ƴan daba.

An kama waɗanda suka kashe miji a gaban matarsa.
Magidanci Ya Rasa Ransa Yayin Kokarin Ceton Matarsa Daga Yan Daba a Bauchi Hoto: leadership
Asali: UGC

Leadership ta ruwaito cewa ƴan daban sun yi yuƙurin ƙwace masa mata, garin kare daraja da martabar matarsa suka kashe shi a kauyen Bazai, ƙaramar hukumar Shira a jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da CoS na shugaban majalisar dokokin Adamawa, sun turo saƙo mai tada hankali

Rahotanni sun nuna cewa ƴan daban su biyu, Awalu Idi, da Habibu Buba sun tare mutumin tare da matarsa yayin da suke hanyar komawa gida daga wurin Maulidi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce da suka tare su, ƴan daban sun umarci mijin ya wuce ya bar musu matarsa, ya nuna musu ba zata saɓu ba, ba zai bari a ci mutuncin mai ɗakinsa ba.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce waɗanda ake zargin sun yi yunƙurin kwace matar daga hannun mijinta na sunnah, Ibrahim Ahmad, wanda ya zama marigayi, amma ya cije ya ƙi yarda.

Kakakin ƴan sandan ya ƙara da cewa, "Daga nan ne suka masa taron dangi, suka lakaɗa masa duka da sanduna, sanadin haka ya samu rauni a cikin kansa"

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun tare babbar hanya a Zamfara, sun halaka mutane da dama tare da sace wasu masu yawa

SP Wakili ya ce an yi gaggawar kai mutumin babban asibitin Yana amma Likitoci suka tabbatar da rai ya yi halinsa.

A rahoton Daily Post, kakakin ƴan sandan ya ce:

“Yayin da aka zurfafa bincike, wadanda ake tuhumar sun amsa laifin aikata wannan ɗanyen aiki. Har yanzu dai ana ci gaba da bincike, idan aka ƙarƙare za a gurfanar da su a Kotu."

Shin sojoji zasu kifar da gwamnati a Najeriya?

A wani rahoton na daban Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya kore yiwuwar juyin mulki a ƙasar nan.

Yayin wata ziyara da ya kai hedkwatar sojoji a Patakwal, CDS ya ce sojojin Najeriya zasu tsaya tsayin daka wajen kare tsarin demokuraɗiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262