“Ni Ba Waliyyi Bane, Najeriya Ba Ta da Matsala”, In Ji Peter Obi
- Game da halin kuncin da Nigeria take ciki, Peter Obi na ganin cewa rashin nagartattun shugabannni da rashin bin diddigi ne ya jawo hakan
- Jagoran jam'iyyar LP, a wata makala da ya gabatar a Benin, jihar Edo, ya kuma ce Nigeria na da arzikin albarkatun kasa, bai kamata tayi talauci ba
- Haka zalika ya yi nuni da cewa Nigeria na dauke da mutane masu basira, akwai bukatar a basu dama domin su baje baiwar da Allah yayi masu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Benin, Edo - Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar LP, Peter Obi, ya bayyana cewa shi ba waliyyi bane, amma ba ya tunanin akwai wata matsala da ke damun Nigeria.
Ya yaba wa kasar kan irin albarkatun da take da su, musamman na ma'adan kasa, kyakkyawan yanayi, arziki ta ko ina, da kuma nagartattun mutane.
Obi ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da wata makala a taron tattaunawa kan tsare-tsare na Edo, da aka gudanar a dakin taro na cibiyar Bishop Kelly Pastoral a Benin, jihar Edo, a ranar Alhamis, 2 ga watan Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Obi yace:
"Ni ba waliyyi bane, kuma ni ba mai laifi bane. Ban taba aikata wani abu da ya zama laifi ba. Na yiwa jihata (Anambra) aiki, kuma na yi aiki a kamfanoni masu zaman kansu. A yau, muna fuskantar talauci a Nigeria. Ma damar ba ka da wani shiri, to ka shirya faduwar ka ne."
"Babu wata matsala da ke damun Nigeria. Nigeria na da duk wani abu da ake bukata, ta fuskar kasa, yanayi, albarkatun kasa, kuma tana da jajurtattun mutane da suka yi fice a duniya, sai dai abu daya da Allah bai ba Nigeria ba shi ne shugaba na-gari. Da ace muna da shuwagabanni na-gari, da munfi haka."
"Babu dalilin da zaisa ace ana talauci a Nigeria" - Peter Obi
Obi ya kuma alakanta halin da Nigeria take ciki da rashin shugaba na-gari, a ganinsa, shugabanci ne kawai abu daya da idan aka yi dacensa Nigeria za ta zama abar alfahari a nan gaba, Legit ta ruwaito.
Ya ce:
"Kasa kamar Nigeria, ba ta da wani dalili da za ace ana talauci, sai dai hakan ta faru saboda rashin nagartaccen shugaba. Muna da jajurtattun mutane da suka yi saura a Nigeria."
"A yau muna da shugabanci ne kawai da ya mayar da hankali kan almubazzaranci ba tare da wani aikin azo-a-gani ba. Amma da zaran ka bude kofofin sarrafa sabbin abubuwa, to za ka samar da ayyukanyi ga mutane"
Taron, wanda aka yi masa take da "Tsarin siyasar Nigeria: Hanyar ci gaba ga jihar Edo," ya jinjinawa shugaban jam'iyyar LP, Julius Abure, tare da samun halartar manyan mutane da suka hada da tsohon gwamnan jihar Abia, Alex Otti.
Babban mai jawabi a taron, Dr Yunusa Tanko, ya nuna yakininsa na cewar Peter Obi zai iya zama shugaban Nigeria, lokaci ne kawai zai tabbatar da hakan.
Nigeria ta shiga cikin matsanancin hali - Peter Obi
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya ce a halin yanzu Nigeria na cikin rudani kuma tana bukatar kwararru irinsa domin ceto rayuwarta.
Obi ya yi wannan jawabi ne a wani shirin ‘The Morning Show’ a gidan talabijin na Arise, inda ya yi jawabi a kan tambayoyin da ke tattare da dambarwar dake tsakanin jam’iyyarsa da jam’iyyar New Nigeria Peoples Party.
Asali: Legit.ng