Dalilin Cusa Sayen Jirgin Ruwan N5bn a Kasafin Kudin da Tinubu ya yi - Aso Rock

Dalilin Cusa Sayen Jirgin Ruwan N5bn a Kasafin Kudin da Tinubu ya yi - Aso Rock

  • A sakamakon maganganu da su ka yi a kan jirgin ruwan da ake son saya, Fadar shugaban kasa ta yi wa al’umma karin haske
  • Mista Bayo Onanuga ya fitar da jawabi ya na mai cewa jirgin da ake magana na sojojin ruwa ne wanda ake son saye tun tuni
  • Hadimin na Bola Tinubu ya ce gwamnatinsu ta gaji sayen jirgin ne daga gwamnatin baya saboda a iya inganta tsaro

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Fadar shugaban kasa ta fitar da jawabi a sakamakon surutan da jama’a su ka rika yi a kan sayen jirgin ruwa a kasafin kudin 2023.

Bayo Onanuga a matsayinsa na Mai taimakawa shugaban kasa a yada labarai da dabaru ya yi karin-haske kan batun a dandalin Twitter.

Kara karanta wannan

A bar batun man fetur; Tinubu ya fadi inda Najeriya za ta koma samun kudin shiga

Bola Tinubu
Bola Tinubu ya yi maganar jirgin ruwa Hoto: @Ajuri Ngelale
Asali: Twitter

Jawabin Bayo Onanuga a madadin Bola Tinubu

"Da farko mu na so mu bayyana cewa shugaban kasa ya na girmama ra’ayin ‘Yan Najeriya a kan abubuwan da su ka shafi al’umma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Saboda haka mu ga muhimmancin warware rashin fahimtar da aka samu a lamarin.
1. Jirgin shugaban kasa da aka gani a kasafin kudi jirgin aikin sojojin ruwa ne, ba na amfanin shugaban kasa. Ana kiransa jirgin shugaban kasa ne saboda manyan matakan tsaro da ke tattare da shi.
2. Tsohuwar gwamnati ta nemi shigo da jirgin sojojin ruwan. Shugaba Tinubu ya saba fada cewa gwamnatinsa cigaba ce domin ya gaji alherai da sharrorin gwamnatin baya.
3. Biyan kudin jirgin ruwan ya na cikin bukatun da shugaban sojojin ruwa ya gabatarwa Ma’aikatar tsaro. Jimillar kudin ya wuce N200bn wanda daga ciki shugaban kasa ya amince da N64bn.
4. Shugaban kasa Tinubu a shirye yake wajen tsare kasarmu da ruwanmu. Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancinsa ta na kashe karin kudi domin samun mai da gas, da tattalin arzikin ruwa.

Kara karanta wannan

Shin Tinubu bai nemi a siya ma sa jirgin ruwa na alfarma? Kakakin Shugaban ya yi bayani

- Bayo Onanuga

A karshen jawabin kamar yadda Olusegun Dada ya wallafa a shafinsa, shugaban kasar ya ce ya san halin da ake ciki kuma zai kawo sauki.

Da kasafin ya je gaban majalisa, an soke shirin sayen jirgin domin bunkasa ilmi.

Tinubu: Za a koma samun kudin ta ma’adanai

Yadda fetur ya zama mafi girman hanyar samun kudin shiga, labari ya zo cewa Bola Tinubu ya ce haka za ayi da bangaren ma’adanai.

A wani jawabi da ya gabatar, Tinubu ya ce ma’adanai za su taka muhimmiyar rawa wajen farfado da tattalin arziki da samar da ayyuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng