Sarkin Musumai Ya Maida Martani Ga Masu Cece-Kuce da Sukar Gayyato Zakir Naik Zuwa Najeriya

Sarkin Musumai Ya Maida Martani Ga Masu Cece-Kuce da Sukar Gayyato Zakir Naik Zuwa Najeriya

  • Sarkin Musulmai ya maida martani ga masu sukar ziyarar da Dakta Zakir Naik ya kawo Najeriya tare da ɗansa
  • Alhaji Sa'ad Abubakar III ya ce Musulmai na da damar da zasu gayyato ɗan uwansu Musulmi domin wata muhadara
  • Shahararren Malamin wanda duniya ta san da zamansa ya halarci makon Sheikh Usman Ɗan Fodiyo na 10 a jihar Sakkwato

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ranar Alhamis ya ce Musulmi na da hakkin gayyato dan uwansu Musulmi domin wata mu'amala.

Sarkin Musulmai tare da Dakta Zakir Naik.
Zakir Naik: "Muna da damar gayyato dan uwanmu Musulmi" Sultan Ya Maida Martani Hoto: Dr. Zakir Naik
Asali: Facebook

Sultan ya gayyaci fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da duniya ta sani, Dakta Zakir Naik, domin ya halarci makon Sheikh Usman Ɗan Fodiyo karo na 10 da aka ƙarƙare ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Babbar nasara: Luguden wutar sojojin Najeriya ya halaka ƴan ta'adda sama da 160 a jihohin arewa 2

Sai dai zuwan Zakir Naik Najeriya bisa gayyatar sarkin Musulmai ya haddasa cece kuce da suka daga ɓangarori daban-daban, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sultan ya maida martani

Da yake maida martani ga masu sukar gayyatar Dokta Zakir Naik, Sarkin Musulmi ya ce:

"Musulunci guda ɗaya ne duk inda kaje a duniya, a matsayin Musulmai muna da dama da haƙƙin gayyato ɗan uwanmu Musulmi ya mana nasiha. Na haɗu da Zakir Naik shekaru 11 da suka gabata."
"Jihar Sakwato na farin ciki da zuwanka, mu musulmai ne kuma muna alfahari da kasancewar mu Musulmai, addini muke wa aiki ba wani mutum ba."
"Allah ya halicce mu a matsayin musulmi kuma babu wanda ya isa ya canza hakan. Muna ƙara godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya yo mu Musulmi”

Sultan ya yi wannan martani ne yayin da yake jawabin rufe taro wanda ya gudana a cibiyar taro ta ƙasa da ƙasa da ke cikin birnin Sakkwato.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun yi fatali da tsagin Atiku, sun koma goyon bayan shugaba Tinubu kan abu 1 tak

Sarkin Musulmin ya ƙara da cewa Sheikh Zakir Naik ya samu damar wayar da kan Musulmai da waɗanda ba musulmai ba kan abin da Musulunci ya kunsa a wannan ziyara.

Zakir Naik Ya Sha Suka

A wani rahoton kuma Malamin addinin Musulunci Zakir Naik ya sha suka a wajen wasu 'yan Nigeria saboda kiran sojojin saman Nigeria 'Sojojin Mulunci'

Zakir Naik ya ziyarci Nigeria ne domin gudanar da wasu karatuttuka da wa'azi a garuruwa daban daban na kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262