Bahaya a Fili: Gwamnatin Jihar Arewa Ta Kashe Naira Miliyan 500 Don Gina Bandakai, Ta Fadi Wurare
- Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana irin makudan kudade da ta kashe don samar da bandakai a wurare da dama don rage bahaya a fili
- Kwamishinan Ruwa a jihar, Ibrahim Hannungiwa shi ya bayyana haka a jiya Laraba 1 ga watan Nuwamba a Dutse babban birnin jihar
- Ya ce gwamnatin ta kashe naira miliyan 500 don samar da ingantattun bandakan bahaya a asibitoci da kasuwanni da tashoshin mota
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Jigawa – Gwamnatin jihar Jigawa ta ce ta kashe makudan kudade har naira miliyan 500 don samar da bandakai.
Kwamishinan Ruwa a jihar, Ibrahim Hannungiwa ya ce sun bandakan a makaranti da kasuwanni da asibitoci da kuma tashoshin mota, Legit ta tattaro.
Nawa Jigawa ta kashe kan samar da bandakan bahaya?
Hannungiwa ya bayyana haka ne a jiya Laraba 1 ga watan Nuwamba a birnin Dutse da ke jiharJigawa, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan ya ce an dauki wannan mataki ne don samun da lafiya da hana yawan yin bahaya a fili.
Ya kara da cewa jihar ta himmatu wurin tabbatar da kawo karshen hana yawan bahaya a fili zuwa shekarar 2025.
Wane mataki Jigawa ta dauka kan bahaya a fili?
Ya ce:
“Mun kafa kwamiti da zai kula da wannan tsari da zai samar da ingantattun bandakai a wurare da dama da kuma kan manyan hanyoyi.
“Gwamnatin jihar takokari sosai wurin wayar wa jama’a kai kan amfani da bandakai musamman a yankunan karkara.
“Jigawa ita ce ta farko da aka ayyana kawo karshen bahaya a fili da Kungiyar UNICEF ta yi.
Hannungiwa ya ce UNICEF ta nada Gwamna Umar Namadi matsayin jakadan kungiyar ta wannan bangare.
Jigawa ta ware naira biliyan 2 don gina makarantun almajirai
A wani labarin, Gwamnatin jihar Jigawa ta ware makudan kudade don gina makarantun almajirai na zamani a jihar.
Gwamnatin ta ware har naira biliyan 2.8 za a zuba su a tsarin ilimin bai daya na BESDA don inganta ilimi.
Kakakin gwamnan, Sagir Musa shi ya bayyana a ranar Laraba 1 ga watan Nuwamba inda ya ce za a gina su a masarautu guda biyar na jihar.
Asali: Legit.ng