Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Ware N2.8bn Domin Gina Makarantun Almajirai
- Gwamnatin jihar Jigawa ta ware N2.8bn domin gina makarantun da Almajirai za su riƙa yin karatun zamani a jihar
- Mai magana da yawun gwamnan, Sagir Musa wanda ya sanar da shirin ya ce za a gina makarantun ne a cikin masarautu biyar na jihar
- Gwamnatin ta jihar Jigawa ta kuma ɗauki malaman makaranta har mutum 3,000 domin magance matsalar rashin isassun malamai a jihar
Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi
Jihar Jigawa - Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sama da Naira Biliyan 2.8 domin gina makarantun tsangaya na Almajirai na zamani a cikin masarautun jihar guda biyar.
Kuɗaɗen da aka amince da su wani ɓangare ne na shirin samar da ingantaccen ilmin bai ɗaya na BESDA, cewar rahoton Premium Times.
Mai magana da yawun gwamnan jihar, Sagir Musa ne ya sanar da wannan matakin bayan taron majalisar zartarwa na jihar wanda gwamna Umar Namadi ya jagoranta a ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamban 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin ya ce makarantun za su ɗauki akalla ɗalibai 12,000 idan an kammala su.
Akwai yara da yawa marasa zuwa makaranta a Jigawa
Jihar Jigawa ce ta biyar a yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya bayan jihohin Bauchi, Kebbi, Katsina da kuma Kano, a cewar hukumar kula da ilimi da kimiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO.
Akwai kimanin yara 784,391 da basa makaranta a jihar. Yawancin yaran da ba sa zuwa makaranta a Jigawa Almajirai ne, waɗanda ba a sanya su a makarantar Boko.
Ko a kwanakin baya, Gwamna Umar Namadi ya nuna kuɗirinsa na mayar da wasu makarantun tsangaya zuwa na makarantun zamani domin koyar da ilmin Boko, rahoton Leadership ya tabbatar.
Kakakin gwamnan ya bayyana cewa jimillar kuɗaɗen da suka kai N2,851,797,098 za a yi amfani da su biyan bashin alawus ɗin wata biyar na masu gudanar da cibiyoyin Almajirai da yara mata.
Tun da farko gwamnan ya amince da ɗaukar malaman makaranta 3,000, domin magance ƙarancin malamai a jihar.
Kwankwaso Zai Taimaki Almajirai
A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya sanar da sabon shirin tallafi ga Almajirai a Kano.
Kwankwaso ya bayyana cewa zai tallafawa Almajiran da suka sauƙe Al-Qur'ani mai girma su yi karatun Boko tun daga firmare har zuwa jami'a.
Asali: Legit.ng