Inda Ranka: Yadda Mutum-Mutumi Ke Aikin ba da Hannu a Titin Abuja Ya Dauki Hankali
- Wani bidiyo da ke yawo ya nuna lokacin da wani mutum-mutumi yake aikin ba da hannu a titin Abuja, babban birnin tarayyar kasar
- An wallafa bidiyon ne a dandalin X kuma wasu mutane da suka gan shi sun ce ya yi kama da mutum ne ya saka rigar
- Sai dai kuma, direbobi da suka ga mutum-mutumin sun bi umurninsa yayin da yake tsaye a tashar yan sanda tare da nuni da hannunsa
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Abuja - An rahoto cewa an gano wani mutum-mutumi yana ba da hannu a wani titin Abuja mai cike da cunkoson ababen hawa.
A cikin wani bidiyo da aka wallafa a soshiyal midiya, an gano mutum-mutumin da ke tsaya a tashar yan sanda kan hanyar inda yake ba ababen hawa hannu.
Bidiyon wanda @XBrianDennis ya wallafa, ya nuna cewa wasu mutane suna ta kallon mutum-mutumin cike da mamaki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutum-mutumi yana ba da hannu a titin Najeriya
Masu ababen hawa da ke wucewa sun yi biyayya ga mutum-mutumin sannan suka bi umurninsa sai kace wani mutum.
Bidiyon ya ja hankalin wasu mutane inda wasu suka ce mutum-mutumin ya yi kama da mutum ne ya saka rigar. Da yake wallafa bidiyon, Xbrianya ce:
"Tunda mutanen Abuja ba za su yi biyayya ga fitilun da ke kula da titi ba, VIO sun kawo wani mutum-mutumi domin ba da hannu a titi."
Kalli bidiyon a kasa:
Martanin jama'a yayin da mutum-mutumi ke ba da hannu a titin Abuja
@XBrianDennis ya ce:
"Sun mayar da 'Optimus Prime' mai ba da hannu a titi."
@HomieSlam ta yi martani:
"Wasu lokutan na kan yi mamakin dalilin da yasa yake da wahala tsayawa na mintuna 3-5 a wajen fitilar titi domin hana cunkoson ababen hawa da hatsari a hanya."
@IamJohnkelvin ya yi martani
"Bumble Beeya shiga ABuja."
@Senior__001 ya yi martani:
"Bige shi zan yi da mota."
@drteepie ta ce:
"Har mutum-mutumin ya gaji."
Wike zai rusa gine-gine a Abuja
A wani labarin, Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta rushe gine-ginen da aka yi watsi da su a Abuja, yana mai cewa wadannan gine-gine sune mabuyar masu laifi a yanzu.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, ministan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba, yayin da ya gurfana a gaban kwamitin majalisar dattawa don kare naira miliyan 100 da aka warewa Abuja cikin karin kasafin kudin 2023.
Asali: Legit.ng