Shugaban NLC Ya Magantu Kan Yadda Aka Lakada Masa Duka a Imo

Shugaban NLC Ya Magantu Kan Yadda Aka Lakada Masa Duka a Imo

  • Shugaban kungiyar kwadago (NLC) Comrade Joe Ajaero, ya kwashi kashinsa a hannun wasu jami'an tsaro da suka yi awon gaba da shi a Owerri
  • An kama Ajaero a lokacin da ya ke shirin jagorantar ma'aikatan jihar Imo gudanar da zanga-zangar nuna rashin goyon baya ga gwamnatin jihar
  • Bayan samun 'yanci, an garzaya da Ajaero zuwa asibiti domin duba lafiyarsa, sakamon raunukan da ya samu a hannun jami'an

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Owerri, jihar Imo - Shugaban kungiyar kwadago (NLC), Comrade Joe Ajaero, ya labarta yadda ya ci dukan tsiya a hannun jami'an tsaron da suka yi awon gaba da shi a ranar Laraba.

Ajaero ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da ya karade kafofin watsa labarai a ranar Alhamis, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaban NLC ya shiga yanayi, za a fitar da shi zuwa kasar waje neman lafiya

Gwamna da shugaban kwadago na jihar Imo
An lakadawa shugaban kwadago dukan tsiya saboda yunkurin yin zanga-zanga Hoto: Hope Uzodimma, Inibehe Effiong
Asali: Facebook

Jawabin Ajaero kan yadda aka kama shi da lakada masa duka

A cikin bidiyon, anji Ajaero yana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Idan aka ce tsawaita dokar kotu, kowa dai ya san dokar kotu na da wa'adi, idan kuma sabuwar doka ce kotun ta bayar, to wannan abu ne na daban.
"Ba sa iya tsawaita dokar kotun; tana da wa'adi na mako daya zuwa biyu ne kawai. Me ya hana ba a bayar da wani sabon umurnin ba? Sun boye takardar ne; sun boye ta a tsakanin su kawai.
"Ya tambaye ni wai na san da cewa za su iya hukunta ni da hujjojin da su ke da su a hannu? Na ce masa, kotun dai da ta bayar da wannan umurnin ita kadai ce za ta iya hukunta ni; ba ku da wani hurumi na hukunta ni haka kawai ba gaira ba dalili.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da aka kwashi shugaban NLC Ajaero zuwa asibiti, cikakken bayani

"In takaita zance, sai da na sha dan karan duka a wajensu, ina ga Allah ne kawai yasa zan yi tsawon rai, amma irin wannan dukan, da sai dai kuji ana wani labarin na daban."

- Joe Ajaero

Dalilin da yasa aka yi awon gaba da Joe Ajaero

Akwai rahotannin da suka bayyana cewa an yi awon gaba da Joe Ajaero daga garin Owerri, inda ya ke shirye shiryen jagorantar ma'aikata gudanar da wata zanga-zanga akan gwamnatin jihar.

An ruwaito cewa Ajaero na tsaka da shirin gabatar da jawabi ga ma'aikatan jihar Imo a sakatariyar NLC, wasu jami'an tsaro dauke da makamai suka mamaye sakatariyar, inda suka yi awon gaba da shi zuwa wani waje da ba a sani ba.

Hakan kuwa ya faru a sa'ilin da Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda (IGP), Kayode Egbetokun, ya isa jihar domin gudanar da bikin sallamar manyan jami'an rundunar 'yan sanda a dakin taro na Landmark da ke Owerri.

Kara karanta wannan

Kungiyar NLC ta tura gargadi daya rak ga gwamnati da zai dagula kasar, ta bayyana dalili

Me ya faru bayan da aka sako Comrade Ajaero?

Kwatsam kuma, sai aka ga bayyanar shugaban kungiyar ta NLC fuskarsa duk ta kumbura da kuma alamun raunuka, bayan da ya kubuta daga hannun jami'an hukumar 'yan sanda.

Haka zalika an garzaya da shi asibitin gwamnatin tarayya na Owerri domin duba lafiyarsa. Kamar yadda majiya ta tabbatar, an kama Ajaero ne bisa umurnin gwamnan jihar, Hope Uzodimma, bisa shirinsa na jagorantar ma'aikata yin zanga-zanga a jihar.

Jami'an Tsaro Sun Cafke Shugaban Kungiyar NLC, An Bayyana Dalili

Jami'an tsaro sun kama shugaban Kungiyar Kwadago (NLC), Joe Ajaero a Owerri babban birnin jihar Imo, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Daruruwan jami'an 'yan sanda dauke da makamai sun kama Ajaero ne a sakatariyar kungiyar inda su ka tafi da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.