An Warware Rawanin Sarkin Hausawa, Haruna Maiyasin Bisa Zargin ya Raina Sarkin Yarbawa Olubadan
- An dakatar da Sarkin Sasa, sakamakon kama shi da laifin nuna rashin ladabi ga Sarkin Hausawan kasar Ibadan
- Hakazalika, Sarki Haruna Maiyasin, ya na kulle-kullen tunbuke rawanin wasu masu sarauta tare da nada wasu ba bisa ka'ida ba
- Dakatar da Maiyasin zai dakile barkewar rikici a tsakanin al'ummar Hausawa kamar yadda ya faru a wasu garuruwan a lokutan baya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Oyo - An dakatar da Sarki Sasa, Haruna Maiyasin, da ke mulkar wani yanki na Hausawa da ke jihar Oyo, bisa zarginsa da 'zagon kasa' da kuma nuna rashin ladabi ga basarake Olubadan na kasar Ibadan.
An zarge shi da nade-naden mukaman sarauta ga mutane ba tare da sahalewar Sarkin Hausawan kasar Ibadan ba.
Wannan matakin na tunbuke rawanin Sarkin Sasa, ya biyo bayan wani zama da al'ummar Hausawa suka yi a ranar Laraba, bisa jagorancin Sarkin Hausawa na kasar Ibadan, Alhaji Ali Zungeru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gudanar da wannan taron ne a fadarsa da ke Sabo, Karamar hukumar Ibadan ta Arewa maso Yamma, da ke jihar.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa basarake Olubadan na kasar Ibadan, Oba Lekan Balogun, ya taba yin gargadi, kan cewar Sarkin Hausawan kasar Ibadan ne kadai yake kallo a matsayin shugaban al'ummar Hausawa a kaf fadin garuruwan da ke karkashin masarautarsa.
La'akari da cewa hatta Oba Balogun ya yi magana kan hakan, bayan wata takardar korafi da Sarkin Hausawan kasar Ibadan, Zungeru ya aike wa masarauta a ranar 18 ga watan Oktoba, 2023, cewar yana zargin Maiyasin (Sarkin Sasa) na gudanar da wasu ayyuka na tayar da zaune tsaye a yankin sa.
Jawabin Sarkin Hausawan kasar Ibadan kan wannan rikici
A jawabin Zungeru bayan kammala taron, ya yi nuni da cewa, ci gaba da zaman Maiyasin a matsayin Sarkin Sasa na iya kunna wata wutar rikici a yankin.
Yace:
"A zamanin mulkin yayana, Shuaibu Dikko III, a shekarar 1983 ne aka nada Maiyasin a matsayin Sarkin Sasa, da aka fi sani da Baale a kasar Yoruba domin gudanar da mulki da nufin samar da zaman lafiya, dai-daito da hadin kai tsakanin Hausawan da ke zama a yankin Sasa
"Sai dai, abun bakin cikin shi ne, Sarkin Sasa yanzu ya fara daukar matakan da ke son rusa zaman lafiyar da ake yi a jihar, ta hanyar yin nade naden sarauta ba tare da sahalewar Sarkin Hausawa na kasar Ibadan ba.
"Hakazalika, akwai zargin wani shiri da yake yi na tsige Sarkin Hausawa a Akinyele, Ado Sule da shugaban 'yan tirela, Yaro Abubakar, wadanda Zungeru ne ya nada su, wanda hakan na iya haddasa rikici. A kula, shi kanshi Maiyasin, yana karkashin Zungeru ne, don haka ba shi da ikon tsige wani daga mukaminsa."
Hukuncin da aka dauka kan mai gundumar Sasin
Domin gujewa duk wani rikici tsakanin al'ummar Hausawan, kamar yadda hakan ta taba faruwa a Sabo-Sagamu, Sabo-Ile-Ife da kuma na baya bayan nan a garin Sasa da ke karamar hukumar Akinyele, Zungeru, sarkin hausawa na kasar Ibadan da duk 'yan majalisarsa, suka dakatar da Maiyasin daga sarautar Sarkin Sasa.
Kuma dakatarwar an yi ta ne saboda rashin nuna ladabi ga masarautar Olubadan ta kasar Hausa da kuma yin nade naden sarauta ga mutane ba tare da sahalewar Sarkin Hausawan Ibadan ba.
Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ahmad Zungeru ya riga mu gidan gaskiya
Alhaji Ahmad Dahiru Zungeru, Sarkin Hausawan Ibadan ya kwanta dama kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.
Rahotanni sun bayyana cewa sarkin ya rasu ne da misalin karfe 9 na daren ranar Lahadi a gidansa da ke Unguwar Sabo, a Ibadan babban birnin jihar Oyo bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.
Asali: Legit.ng