Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ahmad Dahiru Zungeru ya kwanta dama
- Allah ya yi wa Mai Martaba Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ahmad Dahiru Zungeru rasuwa
- Sarkin ya rasu ne a daren ranar Lahadi a gidansa da ke Unguwar Sabo a birnin Ibadan bayan gajeruwar rashin lafiya
- Majalisar Masarautar Hausawan Ibadan ta tabbatar da rasuwa sarkin tare da kafa kwamiti na musamman don jana'izarsa
Alhaji Ahmad Dahiru Zungeru, Sarkin Hausawan Ibadan ya riga mu gidan gaskiya kamar yadda Independent ta ruwaito.
Aminiya ta ruwaito cewa sarkin ya rasu ne da misalin karfe 9 na daren ranar Lahadi a gidansa da ke Unguwar Sabo a birnin Ibadan babban birnin jihar Oyo bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
Marigayi Alhaji Ahmadu Dahiru Zungeru wanda ya rasu yana da shekaru 76 a duniya ya zama sarkin Hausawan Ibadan ne a ranar 13 ga watan Fabrairun 1992.
Majalisar Masarautar Hausawan Ibadan mai Hakimai sama da 50 ta tabbatar da rasuwar Sarkin wanda ya shafe shekaru 29 a karagar mulki.
Majalisar ta kuma fara shirye-shiryen jana'izar marigayin sarki da za a gudanar a ranar Litinin 26 ga watan Yuli misalin karfe 2 na rana.
Hakazalika, an kafa kwamitoci na musamman da aka dora wa alhakin sanar da rasuwar Sarkin ga Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da Mai Martaba Olubadan na Ibadan Oba Saliu Adetunji da Sarkin Musulmin Yarbawa kuma limamin Ibadan Sheikh Abdulganiyu Abubakar Agbotomokekere da manyan yan siyasa da sauransu game da shirye-shiryen jana'izar.
Tsohon Gwamnan Mulkin Soja Na Jihar Jigawa, Ibrahim Aliyu, Ya Rasu
A wani labarin daban, tsohon gwamnan na mulkin soja na jihar Jigawa, Birgediya Janar Ibrahim Aliyu (mai murabus) ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayin ya rasu ne a ranar Juma'a a Kaduna kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da rasuwarsa cikin wata sanarwa da Habibu Nuhu Kila, mashawarci na musamman ga gwamnan Jigawa a bagaren kafafen watsa labarai ya fitar.
Asali: Legit.ng