Daga Karshe Hukumar EFCC Ta Haramtawa Jami'anta Kai Samame da Daddare

Daga Karshe Hukumar EFCC Ta Haramtawa Jami'anta Kai Samame da Daddare

  • Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya yi umurnin cewa gaba daya rassan hukumar su daina kai samame cikin dare
  • Olukoyede ya ba da umarnin a Abuja a ranar Laraba, 1 ga Nuwamba, a matsayin martani ga wani aiki mai cike da takkadama da jami'an hukumar suka yi a Ile-Ife, jihar Osun
  • Kakakin hukumar yaki da cin hanci da rashawar, Dele Oyewale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Legit.ng ta samu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Osun - Hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC), ta sanar da haramta kai samame cikin dare a Najeriya,

Dele Oyewale, shugaban sashin labarai na hukumar ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Jami'an EFCC sun kama daliban OAU 70 yayin wani samamen cikin dare, sun yi martani

EFCC ta haramta aikin dare
Daga Karshe Hukumar EFCC Ta Haramta Aiki da Daddare Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

Shugaban EFCC ya hana jami’an sa kai samame cikin dare

Ci gaban na zuwa ne a daidai lokacin da ake cece-kuce kan kama daliban jami'ar Obafemi Awolowo University (OAU), Ile-Ife, Osun da yawa a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, yan Najeriya da dama sun sha yin korafi game da samamen da jami'an EFCC ke kai wa cikin dare.

A watan Oktoba, mawaki John Njeng-Ngeng, wanda aka fi sani da Skales, ya yi Allah wadai da samamen da hukumar EFCC ta kai gidansa da misalin karfe 4:00 na asuba.

Mawakin, wanda ya garzaya dandalinsa na X (Twitter a baya), ya bayyana cewa wasu jami’an hukumar EFCC sun kai samame gidansa na Lagas da bindigogi da guduma sannan suka fasa masa kofa tare da kwace wayarsa da na bakinsa.

Sanarwar da EFCC ta bayar na dakatar da ayyukan na cewa:

Kara karanta wannan

Mutum 17 sun mutu yayin da wasu 12 suka tsallake rijiya da baya a hatsarin jirgi a jihar Arewa

“A bisa sabon tsarin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC ta yi nazari a kan kame da kuma bayar da belin wadanda ake tuhuma, Shugaban Hukumar, Mista Ola Olukoyede ya bayar da umarnin dakatar da kai samame a cikin dare a gaba daya rassan hukumar.
"Ya ba da umurnin ne a Abuja a ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamban 2023 don martani ga kamen mutum 69 da jami'an hukumar reshen Ibadan a Ile-Ife, jihar Osun suka yi bisa zarginsu da damfara ta yanar gizo. Tuni hukumar ta saki yawancin wadanda ake zargin wadanda aka dauki bayansu, yayin da za a kammala daukar bayanan wadanda ba a saki ba ba tare da bata lokaci ba.
“Hukumar na son tabbatar wa jama’a cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen bin doka da oda, yayin gudanar da aikin ta."

Jami’an EFCC Sun Kama Daliban OAU

A baya mun ji cewa hukumar Yaki da Cin Hanci (EFCC) ta cafke daliban Jami’ar Obafemi Awolowo 70 a daren jiya Talata a jihar Osun.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kama daliban ne da misalin karfe 2 na dare inda jami’an su ka runtuma cikin dakunan kwanan daliban, Legit ta tattaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng