Jerin Sunaye: EFCC Ta Kama Dalibai 69 Kan ‘Damfara Ta Intanet’ a Ile-Ife
- Hukumar EFCC ta cafke dalibai 69 da take zargi da aikata laifukan da suka shafi damfara ta intanet
- An cafke wadanda ake zargin ne a Ile-Ife, jihar Osun bayan da hukumar ta samu bayanan sirri akan irin laifukan da suke aikatawa
- EFCC ta ce ta kwace manyan motoci masu tsada, wayoyi 190 da kuma kwamfutoci 40 daga hannun daliban
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Osun - Jami'an hukumar EFCC shiyyar Ibadan sun cafke dalibai sittin da tara, 69, da ake zargin su da aikata laifuka na damfara a yanar gizo.
An cafke su ne a ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba, 2023 a rukunin gidaje na Oduduwa da ke Ile-Ife, jihar Osun biya bayan sahihan bayanai da hukumar ta samu na ayyukan damfara da suke aikata wa a yanar gizo.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar EFCC ta dora a shafinta na X (tsohuwar Twitter), inda ta bayyana cewa, bayanan sirri da dama sun alakanta rukunin gidajen Oduduwa da zama mafaka ga masu aikata laifukan damfara ta intanet.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jerin sunayen da EFCC ta cafke a Ile-Ife
Hukumar EFCC ta bayyana sunayen daliban da ta cafke a yayin sumamen da suka hada da:
- Dankuwo Eniola Erioluwa
- Mustapha Monsuru Oluwanisola
- Adeyeye Timilehin Ebenezer
- Toromade Hammed Adedeji
- Busari Abdulazeez Ayodeji
- Adeleye Olumuyiwa Emmanuel
- Oluwasakin Moyosore Favour
- Olubini Pere Michael
- Oluwadara Emmanuel Benny
- Gbadamosi Okikola Omotola
- Okusipe Tobiloba Paul
- Nnekwelugo Enaemeka
- Aghwaritoma Wisdom
- Adesina Gbolahan Khalid, da kuma
- Micheal Olugoke Oluwaseun.
Sauran wadanda hukumar ta cafke da zargin aikata laifukan damfara ta yanar gizon sun hada da:
- Obafemi Joshua Mayowa
- Eronmonsele Anthony Igberaese
- Salau Oluwawumi
- Jaiyeola Yinka Temitope
- Ajayi Ayodeji Olanrenwaju
- Oguntade Oluwabukunmi David
- Abdulmumini Abdulsamad
- Tolulope Oduola Folaranmi
- Kayode Abdulraheem Ajuwon
- Akinyemi Oluwagbenro Aduragbemi
- Ayodeji Olumose Adedeji
- Alawode Femi Segun
- Junaid Hafiz Adeyinka
- Akolade Oladele Sunday
- Oyeniyi Banji Andrew
- Oladusu Lanrinde Morakinyo
- Ojo John Ifeoluwa
- Akwuaka Tochukwu Blaise
- Ogunleye Daniel Ayobami, da kuma
- Adebowale Omodesire Diekola.
Sauran sun hada da:
- Arekemase Olayinka Ridwan
- Ajigbolamu Ayomide Ademola
- Asegun David Damola
- Adibe Elvis Ebubechukwu
- Ohakanu Chidubem
- Adeoye Mayowa Irejah
- Adesokan Charles Adekunle
- Olorunfemi Isaac Oladimeji
- Odeyemi Femi Victor
- Alimi Ajibola Akorede
- Okeke Ifaenyi Francis
- Fawehinmi Ayomide Simeon
- Soniola Olumide Elijah
- Yahaya Isah Salihu
- Daramola Junia Olamide
- Agbabikaka Mojuolaoluwa, da kuma
- Kingsley Ejike Nweake.
Sauran su ne:
- Camara Abdullahi
- Aminu Kehinde
- Bayo Adegoke Iyanuoluwa
- Alao Kolawale Oluwaseun
- Oloruntoba Oluwatosin Adeniyi
- Idowu Philip Oluwaseun
- Maiye Daniel Olasile
- Oyelami Peter OLuwaseyi
- Emmanuel Nsochukwu
- Komolafe Tosin, Praise Izuagie
- Umehidi Obinna
- Olujulo Lucas Ifeoluwa
- Omejeh Stanley
- Latilo Tolu
- Oluwaseun Akinrelere ada kuma Great Onufomah.
Abubuwan da aka kwato daga wajen daliban sun hada da manyan motoci masu tsada, wayoyi 190 da kuma kwamfutoci 40, da sauran su.
Tuni dai wadanda ake zargin sun yi wa hukumar EFCC gamsasshen bayani, kuma za a gurfanar da su gaban kotu da zaran hukumar ta kammala bincike.
Kotu Ta Tasa Keyar Dan Damfara Zuwa Ofishin EFCC Don Karbar Lakca, Ta Gindaya Masa Ka'idoji
Kotu ta tura wani matashi mai suna Ndubisi Success zuwa ofishin Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) don masa lakca na mako guda.
Kotun da ke zamanta a Gwagwalada cikin birnin Tarayya Abuja ta umarci a kai shi ofishin hukumar ne don a koya masa sanin amfanin damfara da kuma rashin amfanita, cewar Legit.ng.
Asali: Legit.ng