Emefiele: Tsohon Gwamnan CBN Ya Kara Shiga Tsaka Mai Wuya, Kotu Ta Gindaya Masa Wa'adi Kan Bashi
- Babbar Kotun tarayya ta bai wa tsohon Gwamnan CBN wa'adi ya bayyana a gabanta kan wasu makudan kuɗaɗe da aka ciyo ba shi
- Hakan ya biyo bayan rashin ganin Emefiele a zaman Kotun na ranar Talata amma lauyansa ya bada uzuri
- Bayan sauraron kowane ɓangare, Kotu ta ɗage zama zuwa ranar 25 ga watan Janairu, 2024, ta jaddada cewa dole ta ga keyar Emefiele
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta bai wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, wa'adin daga nan zuwa ranar 25 ga watan Janairu, 2024 ya bayyana a gabanta.
A rahoton da Daily Trust ta tattaro, Kotun ta gindaya wannan wa'adi ne domin Emefiele ya zo ya mata bayanin yadda aka runtumo wa Najeriya bashin dala miliyan 53.
Da yake yanke hukunci ranar Talata, Alkalin kotun ya sake bai wa Mista Emefiele damar kawo kansa gaban kotu ko kuma ita ta bada umarni a kamo shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda zaman Kotun ya kaya
Wannan ya biyo bayan rokon da lauyansa, Audu Anuga, SAN, ya yi cewa duk kokarin da aka yi domin tsohon gwamnan CBN ya samu zuwa zaman kotu ya ci tura domin har yanzu yana tsare.
Anuga ya yi wa kotun bayanin cewa an shigar da takardar shaidar da ke ƙunshe da dalilin da ya sa bai kamata Kotu ta sa a damƙo Emefiele ba tun ranar 30 ga watan Oktoba, 2023.
A cewar babban lauyan sun yi duk kokarin da ya dace har zuwa ranar Juma’a 27 ga watan Oktoba domin su ga an saki Emefiele bisa umarnin kotu amma hakan bai samu ba.
Anuga ya faɗa wa Kotun cewa tun da kowane ɓangare ya aminta da yin sasanci kuma CBN ya yi sabon gwamna, ya kamata Kotu ta zare hannunta a barsu su sasanta.
Amma mai shari’a Ekwo ya dage cewa dole Emefiele ya bayyana a gaban Kotun a ranar zaman Kotu na gaba.
"Dangane da wanda ake kara na 4 (Emefiele), na sha nanata cewa, shari’ar raini ga Kotu tana bin mutum ko karar na nan ko bata nan," in ji Alƙalin.
Daga nan ne alkalin kotun ya ɗage ci gaba da zaman shari'ar zuwa ranar 25 ga watan Janairu domin ɓangaren Emefiele ya gamsar da cewa bai kamata a bada umarnin cafko shi ba.
FG ta tallafawa ɗaliban FUGUS da aka ceto
A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya ta raba tallafin kuɗi ga ɗalibai mata na jami'ar tarayya da ke Gusau waɗan da aka ceto daga hannun ƴan bindiga.
Kwamishinan jin kai da harkokin rage raɗaɗi na Zamfara, Salisu Musa, ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Talata.
Asali: Legit.ng