Sokoto: Yan Sanda Sun Magantu Kan Rahotannin Kama Yan Bindiga Da Ya Bazu a Dandalin Sada Zumunta
- Jami'an 'yan sanda a jihar Sokoto sun yi martani kan jita-jitar cewa sun kama wasu 'yan bindiga a jihar
- Rundunar ta ce labarin da ake yadawa ba gaskiya ba ne, inda ta bayyana ainihin abin da ya faru
- A ranar Litinin 30 ga watan Oktoba an yi ta yada jita-jitar cewa an cafke wasu 'yan bindiga da dama a jihar
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Sokoto - Rundunar 'yan sanda a jihar Sokoto ta karyata cewa ta kama wasu 'yan ta'adda a karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar.
Kakakin rundunar a jihar, Ahmed Rufai ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a jiya Talata 31 ga watan Oktoba.
Wane martani 'yan sandan su ka yi a Sokoto?
Ahmed ya ce rundunar na sane da labarin da ake yadawa a kafar sadarwa na kama 'yan bindigan inda ya ce ba gaskiya ba ne, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi ta yada wani labari cewa 'yan sanda sun kama wasu kasurguman 'yan bindiga a ranar Litinin 30 ga watan Oktoba a Sokoto.
Daga bisani rundunar ta karyata da cewa kwata-kwata babu kamshin gaskiya a cikin labarin.
Sanarwar rundunar ta ce:
"Wannan lamari ya faru ne bayan wasu mutane tara sun tashi daga kauyen Zangon Tashalawa a karamar hukumar Sabon Birni don halartar daurin auren abokinsu, Yusuf Attahiru.
"Matasan sun yi anko a kan babura yayin da 'yan sa kai su ka tare su da zargin ba su amince da su ba.
"Ba tare da wata gardama ba, 'yan sa kai din su ka kama su."
Wane shawara rundunar ta bai wa jama'a?
Rufai ya ce wannan shi ne abin da ya faru wanda aka yi ta yadawa a kafafen yada labarai cikin kankanin lokaci, cewar Tribune.
Ya kara da cewa:
"Ina son yin amfani da wannan dama, in tabbatar da cewa wadannan matasa ba 'yan bindiga ba ne, kawai su na murnar bikin abokinsu ne.
A karshe, ya shawarci al'umma da su yi watsi da labarin inda ya bukaci su ci gaba a lamuran su na yau da kullum cikin lumana.
Sojoji sun hallaka kwamandan 'yan bindiga a Kebbi
Kun ji cewa, rundunar sojin Najeriya ta yi ajalin wani kasurgumin dan bindiga a jihar Kebbi.
Marigayin mai suna Mainasara ya addabi mutane da kai munanan hare-hare da ya jawo rasa rayuka da dama.
Asali: Legit.ng