Sojoji Sun Yi Ajalin Kasurgumin Kwamandan ’Yan Bindiga, Mainasara a Jihar Arewa

Sojoji Sun Yi Ajalin Kasurgumin Kwamandan ’Yan Bindiga, Mainasara a Jihar Arewa

  • Wani kasurgumin kwamandan ‘yan bindiga a jihar Kebbi ya rasa ransa yayin artabu da jami’an sojin Najeriya
  • Marigayin wanda kwamanda ne kuma kasurgumin dan ta’adda mai suna Mainasara ya rasa ransa a dajin Malekachi/Sangeko
  • Daraktan tsaro na rundunar a Birnin Kebbi, AbdulRahman Usman shi ya bayyana haka a yau Talata 31 ga watan Oktoba a Birnin Kebbi

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kebbi – Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar hallaka kasurgumin dan bindiga da wasu mahara biyu a jihar Kebbi.

Kwamandan ‘yan bindigan da ake kira Mainasara ya gamu da ajalinsa ne yayin farmakin sojoji a dajin Malekachi da Sangeko a karamar hukumar Danko Wasagu.

Sojoji sun yi ajalin kwamnadan 'yan bindiga, Mainasara a jihar Kebbi
Sojoji sun yi nasarar sheke kwamanda Mainasara a jihar Kebbi. Hoto: Nasir Idris/ Facebook.
Asali: Facebook

Yaushe rundunar ta yi ajalin Mainasara a jihar Kebbi?

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke daliban firamare 2 da cinna wa makarantarsu wuta, an bayyana yadda abin ya faru

Sauran wadanda aka hallakan su na daga cikin yaran Mainasara wadanda ke kai farmaki ba kakkautawa a yankunan jihar da dama, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daraktan tsaro a Birnin Kebbi, AbdulRahman Usman shi ya bayyana haka a yau Talata 31 ga watan Oktoba a Birnin Kebbi da ke jihar.

Ya bayyana cewa jami’an na sintiri ne a dazukan da misalin karfe 7:30 na safiyar ranar Litinin 30 ga watan Okotoba inda su ka farmaki kan ‘yan bindigan.

Wane sako rundunar ta tura kan kisan Mainasara?

Ya ce:

“Yayin da ‘yan bindigan su ka yi kokarin tserewa, rundunar ta yi nasarar hallaka biyu daga cikinsu inda aka yi nasarar kwace baburansu da kuma lalata su.

Usman ya ce wannan nasara ta rundunar na da alaka da matakan da Gwamna Nasiru Idris ke dauka ma su tsauri wurin samar da tsaro a jihar.

Kara karanta wannan

Babu inda zan tafi, Atiku ya magantu kan mataki na gaba bayan hukuncin kotun koli

Ya godewa Gwamna Idris da irin goyon baya da ya ke bai wa rundunar sojojio a jihar don dakile matsalar da ta ki ci ta ki cinyewa, PM News ta tattaro.

‘Yan bindia sun hallaka mutum 3 a sabon hari a Kebbi

A wani labarin, akalla mutane uku ne su ka rasa rayukansu a kauyen Kazanna a karamar hukumar Bunza da ke jihar Kebbi.

Mutanen uku sun rasa rayukansu ne bayan mahara sun yi mu su kisan gilla a gundumar Tilli da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.