Wani Ɗan Kasuwa Ya Buƙaci Matarsa Ta Biya Naira Miliyan 1.5 Kafin Ya Sake Ta a Kotun Musulunci

Wani Ɗan Kasuwa Ya Buƙaci Matarsa Ta Biya Naira Miliyan 1.5 Kafin Ya Sake Ta a Kotun Musulunci

  • Wata matar aure mai suna, Zainab Bello, ta buƙaci Kotu ta raba aurenta ta hanyar Khul'i, ta ce a shirye take ta maida wa mijin sadakin da ya biya
  • Magidancin, Nura Ashiru, ya faɗa wa Kotu cewa idan har matar tana son saki to ta ba shi Naira miliyan 1.5 saboda ɓarnar da ta masa
  • Alkali ya ɗage zaman zuwa 8 ga watan Nuwamba, 2023 domin wanda ake ƙara ya gabatar da shaidunsa

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Wani ɗan kasuwa, Nura Ashiru, ya buƙaci matarsa mai neman saki ta hanyar khul'i, Zainab Bello, ta biya shi Naira miliyan ɗaya da rabi kafin ya sake ta.

Ashiru ya gabatar da wannan buƙata ne yayin zaman shari'a a Kotun Musulunci mai zama a Magajin Gari, jihar Kaduna ranar Litinin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wani bawan Allah ta faɗa wa kotu yadda sheɗan ya rinjaye shi ya ɗirka wa budurwarsa Maryam ciki

Shari'ar raba aure a Kotun Musulunci.
Wani mutumi ya nemi N1.5m daga wurin matarsa idan tana son ya sake ta Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Hakan ya biyo bayan karar da Zainab ta shigar da mijinta, inda ta nemi Kotu ta raba aurensu ta hanyar Khul'i, wani tsarin da Musulunci ya yi wanda mata zata maida sadakin da aka biya ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi a gaban Kotu, Ashiru ya ce:

"Matata da jawo mun asara mai ɗumbin yawa, ta lalata mun wayar salula kuma ta sace mun wasu kayayyaki na, na taƙaice muku sai da ta jefa ni cikin mawuyacin hali."

Magidancin ya kuma roƙi Kotun kada ta bai wa matarsa ikon rainon ɗan da suka haifa, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

"Zan maida masa sadakina da ya biya"

Tun da farko, mai shigar da ƙara, Zainab Bello ta shaida wa Kotu cewa a shirye take ta biya Mijinta N80,000 da ya bada a matsayin sadakin aurenta.

Kara karanta wannan

Da ɗumi-dumi: "Ba Tinubu ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa ba" Atiku Abubakar ya yi bayani

Ta kuma roƙi kotu ta bata damar ci gaba da rainon ɗansu ɗan shekara uku a duniya. Ta kuma musanta zargin cewa ta lalata wayar mijinta.

Alkalin kotun, Malam Isyaku Abdulrahman, ya dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Nuwamba domin wanda ake kara ya gabatar da shaidunsa.

Sheɗan ne ya rinjaye ni

A wani rahoton na daban wani bawan Allah ya faɗa wa Kotun Abuja cewa sheɗan ne ya rinjaye shi har ya ɗirka wa budurwarsa Maryam ciki ta haihu.

Yayin da budurwar ta kai shi ƙara kan ya ɗauki nauyin yarsu, Harisu Yahaya ya ce ba shi da kuɗin da zai iya wannan aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262