Wani Bawan Allah Ya Faɗa Wa Kotu Yadda Sheɗan Ya Rinjaye Shi Ya Ɗirka Wa Budurwarsa Maryam Ciki
- Wani bawan Allah ya faɗa wa Kotun Abuja cewa sheɗan ne ya rinjaye shi har ya ɗirka wa budurwarsa Maryam ciki ta haihu
- Yayin da budurwar ta kai shi ƙara kan ya ɗauki nauyin yarsu, Harisu Yahaya ya ce ba shi da kuɗin da zai iya wannan aiki
- Maryam ta faɗa wa Kotu cewa tun da ta haihu N4,000 kacal ta raɓa haɗa ta da uban yarinyar wacce a yanzu ta kai shekara shida
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Wani ɗan kasuwa, Harisu Yahaya, ya faɗa wa Kotun yanki mai zama a Kubwa, babbar birnin tarayya Abuja cewa bai so ɗirka wa budurwarsa, Maryam Muhammad, ciki ba.
A zaman Kotun na ranar Litinin, mutumin ya yi wa Kotu bayanin cewa sheɗan ne ya kai shi ya baro, ya angiza shi har ya yi wa wacce yake so ciki kafin aure.
Yahaya ya yi wannan jawabi ne yayin da yake ƙoƙarin kare kansa a ƙarar da Maryam ta shigar, tana neman a umarci ya riƙa ɗaukar ɗawainiyar ɗiyarsu yar shekara shida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka sha dirama a Kotu
Ya ce ba shi da ƙarfin tattalin arzikin da zai iya biyan kuɗin makarantar yarinyar a makarantar da take karatu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A kalamansa ya ce:
"Nine mahaifin yarinyar kuma bamu yi aure da mamarta ba, sharrin sheɗan ne ya ja na ɗirka mata ciki."
Ita dai mai shigar da ƙara, Maryam ta faɗa wa Alkali cewa ba zata damu ba idan Yahaya ya ɗauki yarinyar ta koma hannunsa da zama.
"Yana da iyaye kuma ɗiyarmu zata iya komawa wurinsu da zama, zan janye ƙarar nan idan ya ɗauki yarinyar nan ta koma wurinsa," in ji ta.
Amma da yake martani kan wannan buƙata, Yahaya ya ce mahaifiyarsa ba zata iya kula da ɗawainiyar yarinyar ba.
Tun da farko, Maryam ta bayyana cewa tunda ta duƙa da haifi yarsu, Yahaya bai damu da ciyar da ita ko ɗaukar nauyinta ba.
A cewarta, "Yahaya ya taɓa bani N2,000 na abinci, ya kuma kara turo mun N2,000 na siya wa ɗiyarmu kayan sallah, amma tun daga nan ya zare hannunsa."
"Ina son Kotu ta umarce shi ya ɗauki nauyin ciyar da yarsa kuma ya biya mata kudin makaranta "
Wane mataki Kotun ta ɗauka?
Alkalin kotun, Mai shari'a Ibrahim Rufa'i, ya umarci Maryam da ta rubuta sabon takardar neman riƙon yarsu, sannan ta zo da ita a zama na gaba, NAN ta ruwaito.
Kotu Ta Raba Auren da Ya Shafe Shekara 9
A wani rahoton kuma Ƙotu ta raba auren shekaru tara tsakanin Balkisu Imam da Nasir Imam kan buƙatar da matar ta nema a jihar Kwara.
Alkalin Kotun ya kuma damƙa amanar kula da ɗan da suka haifa ɗan shekara 8 a hannun matar, kuma mijin ya riƙa daukar nauyinsa.
Asali: Legit.ng