Gwamna Zulum Ya Faɗi Ƙungiyoyin 'Yan Ta'adda Biyu da Ke Barazanar Shafe Taswirar Najeriya

Gwamna Zulum Ya Faɗi Ƙungiyoyin 'Yan Ta'adda Biyu da Ke Barazanar Shafe Taswirar Najeriya

  • Farfesa Babagana Umaru Zulum ya ce matuƙar ba a magance Boko Haram da ISWAP ba, zasu iya shafe taswirar Najeriya
  • Gwamnan ya ce ƙungiyoyin ƴan ta'addan ka iya amfani da sansanonin ƴan gudun hijira a matsayin wurin ɗaukar mayaka
  • A cewarsa, ya kamata a warwarwe ƙuncin rayuwa ta yadda za a hana matasa rungumar aikin ƴan ta'adda

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya ankarar da cewa matsalar ƴan ta'addan Boko Haram na barzanar mamaye lungu da saƙo a ƙasar nan.

Gwamnan ya ce matuƙar ba a yi gaggawar shawo kan ƙuncin rayuwar da ya addabi Arewa maso Gabas ba, akwai yuwuwar rikicin Boko Haram ya yaɗu a ko ina, Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Ma'aikata sun garƙame majalisar dokokin jihar Kano, bayanai sun fito

Gwamna Babagana Umaru Zulum.
Gwamna Zulum Ya Ja Hankali Kan Barazanar da Mayakan Boko Haram a Najeriya Hoto: Professor Babagana Umaru Zulum
Asali: Facebook

Farfesa Zulum ya bayyana cewa ci gaba da zaman sansanonin ƴan gudun hijira a kananan hukumomin jihar Borno illa ce babba domin Boko Haram da ISWAP ka iya maida su wurin ɗaukar mayaƙa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Matsayin jihar Borno a taswirar Najeriya yana da matukar muhimmanci a gare mu baki daya. jihar Borno ta haɗa iyaka da ƙasashen Chadi, Kamaru da Jamhuriyar Nijar."
"Iyakokinmu suna da yawa don haka tabbatar da tsaro a shiyyar Arewa maso Gabas tamkar tabbatar da tsaron kasar nan ne baki daya."

Zulum ya faɗi haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin kwamitin gudanarwa na hukumar raya Arewa maso Gabas (NEDC) da aka naɗa a gidan gwamnatin Borno da ke Maiduguri ranar Litinin.

Abin da na hango - Zulum

Ya ci gaba da cewa:

“Yayin da Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya da sauran su ke fama da ‘yan bindiga, garkuwa da mutane, da sauran su, mu a nan Boko Haram ne da ISWAP suka addabe mu."

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun halaka babban limami a jihar Borno

"Gara mu shawo kan waɗan nan ƙungiyoyin, ba dan jihar Borno kaɗai ba. Sansanin Boko Haram da ISWAP yana nan a jihar Borno, ya zama tilas a kawar da su."
"Dole ne mu dakatar da matasa shiga cikin Boko Haram da ISWAP, idan ba haka ba, nan gaba kadan, za su mamaye dukkan Najeriya."

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 7

A wani rahoton na daban Wasu miyagun mahara ɗauke da makamai sun aikata aikin.ta'addanci a wasu ƙauyuka guda biyu na jihar Benue.

Maharan waɗanɗa aka kyautata zaton ƴan bindiga ne sun halaka mutum baƙwai a ƙauyen Tse Gamber da wani ƙauye a ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262