Shugaban Ƙaramar Hukuma a Jihar Arewa Ya Mutu a Hannun 'Yan Bindiga, Bayanai Sun Fito

Shugaban Ƙaramar Hukuma a Jihar Arewa Ya Mutu a Hannun 'Yan Bindiga, Bayanai Sun Fito

  • Allah ya yi wa tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ukum, jihar Benuwai, Raymond Erukaa, rasuwa a hannun ƴan bindiga
  • Babban ɗansa da ya tsira, Charles Erukaa, shi ne ya tabbatar da haka, ya ce suna kokarin gano inda aka jefar da gawarsa
  • Ya bayyana cewa masu garkuwan sun karɓi kuɗin fansa a lokuta daban-daban amma suka ƙi sako shi

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Tsohon shugaban karamar hukumar Ukum a jihar Binuwai, Elder Raymond Washima Erukaa, ya rasu a hannun yan bindiga.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ƴan bindiga sun sace marigayi Erukaa daga gidansa da ke ƙauyen Tse-Erukaa, a cikin Zaki Biam a ranar 23 ga Satumba, 2023.

Kara karanta wannan

Da ɗumi-dumi: "Ba Tinubu ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa ba" Atiku Abubakar ya yi bayani

Tsohon shugaban ƙaramar hukuma, Raymond Erukaa.
Benue: Tsohon Shugaban Karamar Hukuma Ya Mutu a Hannun 'Yan Bindiga Hoto: channelstv
Asali: UGC

Ya kasance shugaban farko na karamar hukumar Ukum da aka kafa a 1981 kuma mahaifin tsohon ma'aikacin gidan talabijin na Channels, Charles Erukaa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban dansa da ya tsira, Charles Erukaa, ya tabbatar wa manema labarai a Makurdi cewa dangi sun samu labarin mutuwar mahaifinsu a ranar 27 ga Oktoba, 2023.

Charles ya ce masu garkuwa da mutane sun tsare mahaifinsa har ya mutu na tsawon kwanaki 34 duk da biyan kudin fansa a lokuta daban-daban.

"Abin takaicin ba zamu iya cewa ga ranar da ya mutu ba sabida muna kan bincike don gano wurin da aka tsare shi, da gano gawarsa."
"A yanzu da nake magana da ku bamu kai ga gano gawarsa ba amma mun yi imanin cewa yau komai zai zo ƙarshe," in ji shi.

A cewarsa, baya ga biyan ƙuɗin fansa, masu garkuwan sun kuma tsare ɗan uwansa, Ben Jones Iorbee Erukaa, lokacin da ya tafi ya kai musu kuɗi miliyan ɗaya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka tsohon shugaban karamar hukuma a Benue bayan sace shi na kwanaki

Ya kara da cewa masu garkuwa da mutanen sun bukaci N12m a farkon tattaunawarsu da dangi amma daga bisani suka rage zuwa N10m.

A cewarsa ba a daɗe ba suka sauko zuwa N5m, kuma a lokacin da dan uwansa, Iorbee Erukaa ya tafi kai masu miliyan ɗaya, sai suka tsare shi tare da mahaifinsa mai shekaru 81, har sai da aka ƙara N2m.

An gano gawarwaki 70 a Abia

A wani rahoton kuma Gwamna Alex Otti ya ce an gano gawarwakin mutane sama da 70 a ƙaramar hukuma ɗaya tal da ke jihar Abiya.

Ya yi bayanin cewa gwamnatinsa zata yi duk mai yiwuwa wajen magance matsalar tsaro a faɗin jihar da ke Kudu maso Gabas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262