Yan Ta'addan Boko Haram Sun Halaka Babban Limami a Jihar Borno

Yan Ta'addan Boko Haram Sun Halaka Babban Limami a Jihar Borno

  • Wasu miyagun ƴan ta'adda da ake kyautata zaton mayaƙan ƙungiyar Boko Haram ne sun kai hari a ƙaramar hukumar Kaga ta jihar Borno
  • Ƴan ta'addan waɗanda suka farmaki gidan babban limamin Kaga, sun halaka shi har lahira tare da wani ɗan sakai mutum ɗaya
  • Majiyoyi sun tabbatar da aukuwar harin inda suka ce marigayin shi ne babban limamin Kaga na biyu da ƴan ta'adda suka halaka a cikin watanni biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wakilin Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar fiye da shekara biyar wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Jihar Borno - Wasu mahara da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kashe babban limamin Kaga, Imam Goni Muktar, da wani ɗan sakai a ƙaramar hukumar Kaga ta jihar Borno.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa, ƴan ta’addan da ke cikin mota ƙirar Golf Volkswagen sun kai farmaki a gidan limamin da ke Malamti, a wajen garin Benishek da misalin karfe 12:30 na daren ranar Lahadi, 29 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Miyagun Yan Bindiga Sun Kai Hari a Katsina, Sun Halaka Mutum 3 da Yin Awon Gaba da Wasu da Dama

Mayakan Boko Haram sun halaka babban limami
Mayakan Boko Haram sun halaka babban limami a Borno Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

A cewar wata majiyar rundunar ƴan sakai ta CJTF, yanayin yadda aka kawo harin ya kasance irin na ƴan ta'adda ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda mummunan lamarin ya auku

A kalamansa:

"A daren ranar Lahadi ne wasu ‘yan bindiga da ake zargin ƴan Boko Haram ne suka kai farmaki gidan babban limamin ƙaramar hukumar Kaga, Goni Muktar, sannan suka kashe shi."
"Maharan sun ɗauke ɗaya daga cikin ƴan sakai da ke bakin aiki da ƙarfin tsiya. Wannan shi ne babban limami na biyu da aka kashe a Kaga cikin watanni biyu."

A cewar rundunar CJTF, ba a iya gano musabbabin aukuwar lamarin ba, amma a yau ne za a yi jana'izar marigayin limamin.

'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Halaka Mutum Hudu

A wani labarin kuma, ƴan ta'addan ƙungiyar Boko Haram sun kai wani mummunan harin ƙwanton ɓauna kan matafiya da ke kan titin hanyar Gwoza-Limankara a jihar Borno.

A yayin harin da ƴan ta'addan suka kai, sun halaka mutum huɗu ciki har da wani jami'in soja wanda ke cikin tawagar ayarin motocin ƴan sakai na CJTF da sojoji masu aikin rakiyar matafiya a hanyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng