Abun Tausayi: An Gano Gawarwakin Mutane Sama da 70 a Ƙaramar Hukuma Ɗaya Tal, Gwamna Ya Magantu
- Gwamna Alex Otti ya ce an gano gawarwakin mutane sama da 70 a ƙaramar hukuma ɗaya tal da ke jihar Abiya
- Ya yi bayanin cewa gwamnatinsa zata yi duk mai yiwuwa wajen magance matsalar tsaro a faɗin jihar da ke Kudu maso Gabas
- Gwamnatin Otti ta gano gawarwakin ne a kusa da kasuwar shanu ta Lokpanta, wasu babu kawuna da kuma kwarangwal ɗin mutane
Ahmad Yusuf, na ɗaya daga cikin editocin da ke kawo rahotannin siyasa da harkokin yau da kullum fiye da shekaru biyu da suka shige
Jihar Abia - Gwamnatin jihar Abiya ta gano gawarwakin mutane sama da 50, da wasu gawarwaki sama da 20 da aka cire wa kawuna da ƙwarangwal na mutane da yawa.
Channels tv ta tattaro cewa an gano waɗan nan gawarwaki masu ɗumbin yawa ne a kusa da kasuwar shanu ta Lokpanta a ƙaramar hukumar Umunneochi da ke jihar.
Gwamna Alex Otti ne ya bayyana haka yayin jawabi ga 'yan jarida wanda ya saba yi kowane wata a gidan gwamnati da ke Ummuahia, babban birnin jihar Abiya ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma tabbatar wa al’umma cewa gwamnatinsa ta dukufa wajen ganin ta magance matsalar rashin tsaro ba tare da la’akari ko tsayawa tantance su wa hakan zata shafa ba.
Otti ya ce karuwanci, sana’ar muggan kwayoyi da sauran miyagun laifuka da suka yawaita a kusa da Kasuwar Shanu ta Lokpanta ne ya sa aka kai farmaki kasuwar.
A cewar gwamnan, ko a kwanan nan an rushe wasu gidajen karuwai a Umunneochi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnati ta faɗi sabon tsarin kasuwar
Gwamnan ya bayyana cewa kasuwar Lokpanta za ta zama tana ci a kowace rana kuma za a riƙa bude ta da karfe 6 na safe kuma za a rufe da karfe 6 na yamma.
Ya ce yanzu kasuwar za ta zama kasuwa ce ta gama-gari saboda an ɗauki wani sashi an bai wa dillalan shanu da sauran masu sana’o’i daban-daban.
A cewarsa, yankin Lokpanta ya yi kaurin suna wajen yin garkuwa da mutane da fashi da makami, don haka ne gwamnatinsa ta yanke shawarar maida kasuwar mai ci kowace rana.
Otti ya ce:
"Mun haɗu a abu ɗaya kan kawar da matsalar tsaro a jihar Abia, domin mun san cewa babu wata gwamnati da za ta iya yin nasara wajen fuskantar rashin tsaro, tashin hankali, fashi da kuma garkuwa da mutane ita kaɗai."
Yan bindiga sama da 100 sun mutu
A wani rahoton kuma sojojin saman Najeriya sun halaka 'yan bindiga sama da 100 a wani ruwan bama-bamai da suka yi a iyakar jihohin arewa biyu.
Hedkwatar tsaro ta ƙasa DHQ ta bayyana cewa a cikin mako ɗaya, sojoji sun aika gomman da yan bindiga lahira, sun damƙe wasu.
Asali: Legit.ng