Majalisar Dokokin Jihar Rivers Ta Mika Wa Gwamna Fubara Takardar Shirin Tsige Shi
- Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers da yaƙin da yake yi da majalisar dokokin jihar ya ƙara tsananta
- Rahotanni sun bayyana cewa majalisar dokokin jihar ta miƙa wa gwamnan mai shekara 48 a duniya, takardar shirin tsige shi
- An tattaro cewa gwamnan ya amsa kiran inda ya bayyana a gaban majalisar a ranar Litinin, 30 ga watan Oktoba
Jihar Rivers - Rahotanni da ke fitowa sun tabbatar da cewa majalisar dokokin jihar Rivers ta miƙa wa gwamna Siminalayi Fubara takardar shirin tsige shi.
Wakilin gidan talabijin na Channels Tv ya bayyana hakan a ranar Litinin, 30 ga watan Oktoba, a lokacin da ake watsa shirin safe na kai tsaye mai suna "Sunrise Daily".
Wakilin gidan talabijin na Channels Tv ya ce gwamnan ya isa harabar majalisar ne tare da shugaban masu rinjaye na majalisar, Edison Ehie, wanda kakakin majalisar da wasu ƴan majalisar suka tsige.
Rahotanni sun bayyana cewa Ehie ya kawo cikas a yunƙurin farko na fara shirin tsige gwamnan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa aka tsige shugaban masu rinjaye na majalisar?
Yayin zaman majalisar a birnin Fatakwal, babban birnin jihar, kakakin majalisar, Martins Amaehwule, ya bayyana cewa an tsige shugaban masu rinjayen ne daga muƙaminsa saboda rashin halartar zaman majalisar da yake yi.
Amaehwule ya ƙara da cewa ƴan majalisar kusan 17 ne suka goyi bayan tsige shugaban masu rinjayen, a cewar rahoton Daily Trust.
Magoya bayan gwamnan sun taru a harabar majalisar dokokin jihar, inda suka fara zanga-zangar adawa da tsige shi da ake shirin yi.
Hakan dai na faruwa ne jim kaɗan bayan tashin gobara a harabar majalisar a daren ranar Lahadi, 29 ga watan Oktoba
Har yanzu dai babu tabbas kan ko gobarar na da nasaba da taƙaddamar siyasar, sai dai ana ta raɗe-raɗin cewa an daɗe ana takun saƙa tsakanin Fubara da magabacinsa, Nyesom Wike, wanda a yanzu shi ne ministan babban birnin tarayya Abuja.
Ban Cancanci a Tsige Ni Ba - Gwamna Fubara
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya yi magana kan shirin tsige shi da majalisar dokokin jihar ke shirin yi.
Gwamna Fubara ya bayyaana cewa bai yi wani laifi ba wanda ya cancanci ya ssnya a raba shi da muƙaminsa na gwamnan jihar.
Asali: Legit.ng