Magoya Bayan Gwamna Fubara Sun Dira Majalisar Dokokin Rivers Kan Shirin Tsige Shi

Magoya Bayan Gwamna Fubara Sun Dira Majalisar Dokokin Rivers Kan Shirin Tsige Shi

  • Magoya bayan gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers sun yi dafifi zuwa harabar majalisar dokokin jihar
  • Magoya bayan gwamnan sun yi dafifi zuwa harabar majalisar ne domin nuna adawarsu da shirin tsige gwamnan da majalisar ke yi
  • Hakan na zuwa bayan majalisar dokokin ta tsige shugaban masu rinjaye na majalisar wanda na hannun daman gwamna Fubara ne

Jihar Rivers - Magoya bayan gwamna Siminalayi Fubara sun mamaye majalisar dokokin jihar Ribas a daidai lokacin da ake shirin tsige shi.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa an ga magoya bayan gwamnan suna rera waƙoƙin nuna goyon baya cikin yarensu a safiyar ranar Litinin, 30 ga watan Oktoban 2023.

Magoya bayan Fubara sun dira harabar majalisa
Magoya bayan gwamna Fubara sun dira harabar majalisar dokokin jihar Rivers Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Yayin da suke kewaye da wasu jami’an tsaro masu riƙe da manyan bindigogi, magoya bayan gwamnan sun garzaya zuwa harabar ginin majalisar, lamarin da ya haifar da tashin hankali.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da jami'an tsaro suka yi harbi kan Gwamna Fubara na Rivers

Hakan na zuwa ne dai bayan an tsige Edison Ehie, mai goyon bayan gwamnan a matsayin shugaban masu rinjaye na majalisar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi nuni da cewa Ehie ya kawo cikas tun da farko a ƙoƙarin fara shirin tsige Fubara, wanda ya gaji Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, ƙasa da watanni shida da suka wuce.

Rahotanni sun yi nuni da cewa dangantaka tsakanin Fubara da tsohon gwamna Wike ta yi tsami.

Ban cancanci a tsige ni ba - gwamna Fubara

Gwamna Siminalayi Fubara ya yi magana kan shirin tsige shi daga muƙamin gwamnan jihar Rivers da majalisar dokokin jihar ke yunƙurin yi.

Gwamnan a yayin da yake jawabi ga dandazon magoya bayansa a harabar majalisar dokokin jihar, yabayyana cewa bai cancanci a tsige shi daga muƙamin gwamnan jihar Rivers ba.

Kara karanta wannan

Majalisar dokokin jihar Rivers ta mika wa gwamna Fubara takardar shirin tsige shi

Fubara ya yi nuni da cewa babu wani laifi da ya aikata wanda har zai sanya mambobin majalisar dokokin jihar fara shirin tsige shi daga muƙaminsa na gwamna ba.

Majalisar Dokokin Rivers Ta Sanar da Fubara Shirin Tsige Shi

A wani labarin kuma, majalisar dokokin jihar Rivers, ta miƙa wa gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, takardar fara shirin tsige shi daga muƙamin gwamnan jihar.

Hakan na zuwa ne bayan ƴan majalisar dokokin jihar sun tsige shugaban masu rinjaye na majalisar saboda goyon bayansa ga gwamnan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng