Yan Bindiga Sun Sace Babban Malamin Addini da Wasu Mutum 2 a Taraba

Yan Bindiga Sun Sace Babban Malamin Addini da Wasu Mutum 2 a Taraba

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun yi awon gaba da wani babban fasto na cocin Katolika ta Wukari a jihar Taraba
  • Ƴan bindigan sun sace Rabaran Fr. Thaddeus Terhembe ne a cocinsa da ke ƙaramar hukumar Idi ta jihar
  • Haka kuma rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da sace wasu mutum biyu da ƴan bindiga suka yi a cikin birnin Jalingo, babban birnin jihar Taraba

Jihar Taraba - Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da wani babban malamin adinini, Rabaran Fr. Thaddeus Terhembe na cocin Katolika ta Wukari a jihar Taraba.

Jaridar Channels tv ta kawo rahoto cewa lamarin ya auku ne da sanyin safiyar ranar Lahadi, 29 ga watan Oktoban 2023.

Yan bindiga sun sace fasto a Taraba
Yan bindiga sun yi awon gaba da babban fasto a Taraba Hoto: guardian.com
Asali: UGC

Wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na cocin Katolika ta Wukari, Rabaran Fr John Jerome, ya fitar ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce an sace shi ne a cocinsa ta Saint Ann’s Parish, a Sarkin Kudu cikin ƙaramar hukumar Ibi ta jihar Taraba.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Kazamin Hari FCT, Sun Yi Awon Gaba da Mutane da Dama a Arewa

Sanarwar ta buƙaci mazauna garin da su yi masa addu'ar Allah ya kare shi ya kuma kuɓutar da shi cikin gaggawa, rahoton The Guardian ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sace mutum biyu a birnin Jalingo

An yi garkuwa da mutum biyu a unguwar Gulum da ke Jalingo, babban birnin jihar Taraba, tare da kwashe dukiyoyinsu.

Masu garkuwa da mutanen sun shiga gidan mutanen ba tare da wata fargaba ba, inda suka yi awon gaba da su zuwa cikin daji.

Jami'in hulɗa da jama'a na ƴan sandan jihar Taraba, Abdullahi Usman, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Jirgin ruwa ya kife a Taraba

Wani jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji sama da mutum 100, ya gamu da hatsari a sakiyar rafin Benue a jihar Taraba.

Jirgin mai ɗauke da ƴan kasuwa, mata da ƙananan yara, ya taso daga garin Binnari zuwa ƙaramar hukumar Karim-Lamido ta jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Innnalillahi: Mutane da Dama Sun Mutu Yayin da Wani Jirgi Ya Gamu da Matsala a Jihar APC

Yan bindiga sun halaka mutum biyu a Taraba

A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a kasuwar Didango da ke ƙaramar hukumar Karim-Lamido ta jihar Taraba.

Ƴan bindigan waɗanda ake kyautata zaton mayaƙan wata ƙabila ne sun halaka mutum biyu tare da sace kayayyaki na miliyoyin naira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng