Abubuwa 5 Da Ya Kamata a Sani Game Da Marigayi Ohinoyi na Kasar Ebira, Ado Ibrahim

Abubuwa 5 Da Ya Kamata a Sani Game Da Marigayi Ohinoyi na Kasar Ebira, Ado Ibrahim

Ebira, jihar Kogi - Ohinoyi na kasar Ebira, Alhaji Abdulrahman Ado Ibrahim ya amsa kira mahaliccinsa a ranar Lahadi, 29 ga watan Oktoba.

Ohinoyi na kasar Ebira ya kasance basarake mai daraja ta daya.

Allah ya yi wa Ado Ibrahim rasuwa a ranar Lahadi
Abubuwa 5 Da Ya Kamata a Sani Game Da Marigayi Ohinoyi na Kasar Ebira, Ado Ibrahim Hoto: @a_rufai_jr
Asali: Twitter

Marigayi basaraken ya kasance kan karagar mulki tun watan Yunin 1997.

A wannan rahoton, Legit Hausa ta rubuto abubuwan da ya kamata a sani game da marigayi Ado Ibrahim.

1) Sarkin Ebira na hudu

Ado Ibrahim ya kasance basaraken gargajiya na hudu kuma Ohinoyi na kasar Ebira.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kasance dan Attah na biyu (Ohinoyi a yanzu) na kasar Ebira, Ibrahim Onoruoiza, na daular Omadivi, wanda ya yi sarauta daga 1917 zuwa 1954.

Marigayi Ado Ibrahim ya shafe shekaru 26 a kujerar.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Allah Ya Yi Wa Ohinoyi na Kasar Ebira Ado Ibrahim Rasuwa a Asibitin Abuja

2) Tsohon dalibin makarantar tattalin arziki na Landan da makarantar kasuwanci na Harvard

Ado Ibrahim ya mallaki digiri daga makarantar tattalin arziki na Landan, kasar Birtaniya.

Ya kuma mallaki digiri na biyu daga makarantar kasuwanci na Harvard, kasar Birtaniya, wanda ya samu a 1959.

3) Tsohon dan kasuwa mazaunin Lagas

Biyo bayan mutuwar Ohinoyi Sanni Omolori na daular Oziada a 1997, Ado Ibrahim wanda ya kasance dan kasuwa mazaunin Lagas ya dare kujerar sarautar ta Okene.

Ya dare kujerar sarautar a matsayin basaraken kasar Ebira na hudu a ranar 2 ga watan Yunin 1997.

4) Fadarsa na cikin mafi kyawu a yammacin Afrika

Ibrahim ya gina fadar Azad, wanda ya sakawa sunan daya daga cikin yaransa maza. Fadar na daya daga cikin wadanda suka fi kyawu a yammacin Afrika.

Ya kasance gidan siyasa, tarihi, sarauta da addini ga mutanen Ibira.

5) Mahaifin dan takarar shugaban kasa

Daya daga cikin yaran marigayi Alhaji Ado Ibrahim, Prince Malik Ado-Ibrahim, ya kasance dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar YPP a zaben shugaban kasar Najeriya na 2023.

Kara karanta wannan

Albishir Ga ’Yan Crypto, Abu 1 Ya Sa Bitcoin Ya Tashi a Najeriya, Ajantina da Turkiyya

Prince Malik bai yi nasara ba a zaben shugaban kasar.

Ohinoyi na kasar Ebira ya kwanta dama

A baya Legit Hausa ta kawo cewa Allah ya yi wa Ohinoyi na kasar Ebira, Dr Ado Ibrahim, rasuwa yana da shekaru 94 a duniya.

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, babban basaraken na kasar Ebira ya koma ga mahaliccinsa a safiyar ranar Lahadi, 29 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng