Yadda Wani Mutum Ya Yi Wa Makwabcinsa Duka Har Lahira Saboda N4,500 a jihar Ogun

Yadda Wani Mutum Ya Yi Wa Makwabcinsa Duka Har Lahira Saboda N4,500 a jihar Ogun

  • Wani mutum ya halaka makwabcinsa sakamakon sabani da ya shiga tsakaninsu kan N4,500 a jihar Ogun
  • Wanda ake zargin, Wasiu Oyekan ya naushi marigayin, Ibrahim Lateef a wuya inda ya fadi kasa kansa ya daki kasa
  • Rigima ya fara ne bayan Oyekan ya mika dan marigayi Lateef ga ofishin yan sanda a kan bashin da ya ke binsu na barnar da suka yi masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Ogun - Rahotanni sun kawo cewa wani mutum mai suna Wasiu Oyekan ya yi wa daya daga cikin makwabtansa duka har lahira a kan N4,500 a garin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

An tattaro cewa makwabcin, Ibrahim Lateef, ya mutu ne lokacin da wanda ake zargin ya naushe shi a wuya inda ya fadi ya buga kai a kasa.

Kara karanta wannan

Ana Min Kallon Ba Zan Iya Ba Saboda Na Iya Rawa, Gwamnan PDP

Wani mutum ya kashe makwabcinsa da duka
Yadda Wani Mutum Ya Yi Wa Makwabcinsa Duka Har Lahira Saboda N4,500 a jihar Ogun Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya afku ne a kusa da babban masallacin Juma'a na Kobiti, yankin Kobiti a garin Abeokuta.

Yadda abun ya faru

An tattaro cewa Oyekan wanda ke zaune a yankin Ile-Elewe Family a Kobiti ya zargi dan marigayin da wani yaro da lalata masa bidiyon buga wasanninsa yayin da suke buga wasa a watan Agusta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bukaci a biya shi N9,000 domin ya gyara abun wasan, wanda mahaifin yaron mai shekaru 50 ya ba shi N4,500, tare da alkawarin cika sauran daga baya.

Jinkiri wajen biyan sauran N4,500 din ne yasa Oyekan ya kai dan marigayin ofishin yan sanda.

Wani ganau ya ce:

"Lokacin da mahaifinsa ya dawo gida sannan ya lura cewa Wasiu ya kai dansa ofishin yan sanda, sai ya tafi wajensa kai tsaye kuma yayin da yake kokarin tambayar Wasiu dalilin kai dan nasa gidan yan sanda, sai ya far masa da naushi a wuyansa. Lateef ya fadi nan take sannan kansa ya daki kaa. Ya fara zubar da jini ta hanci da kunne. ya kuma mutu."

Kara karanta wannan

Rarara: Tsohon Hadimi Ya Mayar Wa Mawaki Raddi Mai Zafi Saboda Caccakar Mulkin Buhari

Shaidan ya ce yanzu haka wanda ake zargin yana sashin binciken laifuka na jihar, hedkwatar rundunar yan sanda a Eleweran, Abeokuta.

Lateef, wanda ake kira da Tijuuku, ya mutu ya bar mahaifiyarsa, mata wacce ke shayar da yarinya yar watanni biyu, sauran yaransa da kanne, rahoton The Eagle.

Rundunar yan sanda ta yi martani

Kakakin rundunar yan sandan jihar, Omolola Odutola ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a.

Odutola ya tura wakilin Daily Trust zuwa ga jami’ar yan sanda na Oke-Itoku, CSP Hadiza Abu Oganyi, wacce a karkashinta lamarin ya faru.

DPO din ta kuma tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa ta tura lamarin ga hedkwatar rundunar a ranar da ya faru.

A cewarta, marigayin ya je ya tunkari Oyekan da fada kan kai karar dansa ofishin yan sanda, cewa wannan ne masomin abun.

Shugabar yan sandan ta ce za ta mika cikakken bayani ga kakakin yan sandan kasancewar ba a bata damar yin magana ga manema labarai ba.

Kara karanta wannan

“Wike Na Da Laifinsa”: MURIC Ta Goyi Bayan Gumi Yayin Da Ya Kira Ministan Abuja ‘Shaidani’

Ohinoyi na kasar Egbira ya kwanta dama

A wani labarin kuma, mun ji cewa Allah ya yi wa Ohinoyi na kasar Ebira, Dr Ado Ibrahim, rasuwa yana da shekaru 94 a duniya.

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, babban basaraken na kasar Ebira ya koma ga mahaliccinsa a safiyar ranar Lahadi, 29 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng