Mummunar Gobara Ta Lakume Kayan Miliyoyin Naira a Wata Babbar Ƙasuwa a Jihar Legas
- An samu tashin wata mummunar gobara a wata babbar kasuwa a tsibirin jihar Legas inda ta laƙume kayayyakin miliyoyin naira
- Gobarar ta tashi ne a wasu benaye uku masu hawa uku a kasuwar da ke kan titin Dosunmu a yankin tsibirin na Legas
- Hukumar kashe gobara ta jihar ta samu nasarar kashe gobarar tare da daƙile yaɗuwarta zuwa sauran gine-ginen da ke kasuwar
Jihar Legas - Wata mummunar gobara ta ƙone wasu benaye uku masu hawa uku tare da lalata kadarori na miliyoyin Naira a wata kasuwa da ke kan titin Dosunmu a yankin tsibirin Legas a jihar Legas.
Hukumar kashe gobara ta jihar Legas ta bada rahoton cewa an shawo kan gobarar.
Hukumomi sun tabbatar da aukuwar gobarar
Daraktar hukumar, Margaret Adeseye, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce gobarar da aka bayar da rahoton tashin ta da misalin karfe 8:50 na daren ranar Asabar ta shafi wasu "benaye uku masu hawa uku."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamanta:
"A halin da ake ciki, har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba domin bincike zai bayyana hakan daga baya yayin da gobarar ta shafi kayayyaki iri-iri da suka haɗa da makulli/silinda, kayan ado, da kayan Kirsimeti, da sauran su wadanda ba a iya tantance adadin kuɗinsu nan take ba."
Ta yi nuni da cewa ɗaukin gaggawa da jami'an kashe gobara suka kai a kan lokaci ya taƙaita gobarar a gine-ginen da ke saman benayen.
"Babu wani rahoton rauni ko asarar rai yayin da aka cigaba da gudanar da ayyukan ceto." Ta ƙara da cewa.
Gobara ta laƙume shaguna bakwai
Iftila’in gobara ta cinye wani bangaren babbar kasuwar Watt da ke tsakiyar birnin Calabar a cikin jihar Kuros Riba.
Ƴan kasuwar sun zargi wayoyin wuta da ke rataye a mafi yawan fola-folai da ke tsagaye da kasuwar ne dalilin jawo gabarar.
Gobara Ta Lalata Shaguna 14 a Adamawa
A wani labarin na daban kuma, wata mummunar gobara ta laƙume shagunan hatsi a jihar Adamawa.
Gobarar wacce ta tashi a babbar kasuwar birnin Yola, babban birnin jihar Adamawa, ta laƙume shaguna 14.
Asali: Legit.ng