Nade-Nade a INEC: An Zargi Tinubu da Ba Mambobin APC Mukamin REC
- Ana zargin Shugaba Bola Tinubu da ƙoƙarin murɗe zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ta hanyar naɗa mambobin APC a matsayin RECs na INEC
- Fisayo Soyombo, ya yi wannan zargin a ranar Asabar, inda ya ce ɗaya daga cikin sabbin kwamishinonin na INEC, Etekamba Umoren, tsohon shugaban ma'aikata ne ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio
- A cewar Soyombo, Umoren ya taɓa shiga wata ƙara inda aka tuhumi Akpabio da karkatar da N22bn daga jihar Akwa Ibom
FCT, Abuja - An zargi Shugaba Bola Tinubu da yin aiki gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ta hanyar naɗa mambobin jam’iyyar APC a matsayin kwamishinonin zaɓe (REC) a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).
Fisayo Soyombo, wani ɗan jarida mai bincike a Najeriya, ya yi wannan zargin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Asabar, 28 ga watan Oktoba, inda ya yi zargin cewa shugaban ƙasar na shirin ganin ya mulki Najeriya har zuwa bayan 2027.
Tinubu ya naɗa REC guda 10 na INEC
A farkon makon nan ne dai Shugaba Tinubu ya amince da naɗin kwamishinonin zaɓe guda 10 na INEC waɗanda za su yi aiki na tsawon shekara biyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗan jaridar mai bincike ya yi zargin cewa an ɗauki matakin ne domin kawar da duk wani ɗan adawa daga ɗarewa kujerar shugaban ƙasa a zaben shugaban ƙasa na 2027.
Soyombo ya yi nuni da Etekamba Umoren, wanda sunansa ne na farko a jerin sunayen, inda ya yi zargin cewa na hannun daman shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ne kuma ɗan jam'iyyar APC mai mulki.
Akpabio, Umoren an taɓa gurfanar da su a kotu tare, in ji Soyombo
A cewar Soyombo, Umoren ya shiga cikin wata ƙara inda aka zargi Akpabio da fitar da N22bn daga baitul malin jihar Akwa Ibom kuma da zargin karkatar da kuɗin domin amfanin ƙashin kansa.
Ɗan jaridar ya ce Umorem ya taɓa zama babban sakatare a gidan gwamnatin Akwa Ibom, tsohon shugaban ma'aikatan Akpabio lokacin yana gwamna da kuma sakataren gwamnatin jiha (SSG) a Akwa Ibom.
Wani ɓangare na bayaninsa na cewa:
"Majalisar dattawan da za ta amince ko ƙin amincewa da Umoren, na ƙarƙashin jagorancin ubangidansa Akpabio."
"Koƙarin bayan fage na murɗe abin da masu kaɗa ƙuri'a suka zaɓa a 2027, ya fara shekara huɗu kafin lokacin ya yi!"
Hadiza Bala Usman Ta Caccaki Amaechi
A wani labarin kuma, hadimar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Hadiza Bala Usman ta caccaki tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi.
Hadiza ta buƙaci Amaechi da ya sann cewa ya girma ya daina sharara ƙarya bayan ya yi mata raddi kan wani littafi da ta rubuta.
Asali: Legit.ng