Atiku Ya Halarci Taro Na Musamman Bayan Hukuncin Kotun Koli, Ya Sanya Hotuna

Atiku Ya Halarci Taro Na Musamman Bayan Hukuncin Kotun Koli, Ya Sanya Hotuna

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya halarci daurin auren ɗiyar mukaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Umar Damagum
  • Wannan dai shi ne karon farko da ya bayyana a bainar jama’a tun bayan da kotun koli ta yi watsi da daukaka karar da ya shigar kan nasarar da Shugaba Tinubu
  • Yayin da PDP ta fitar da sanarwar yin Allah wadai da hukuncin da kotun ta yanke, Atiku bai mayar da martani da kan sa kan hukuncin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, a ranar Juma'a, 27 ga watan Oktoban 2023, ya halarci ɗaurin auren ɗiyar shugaban riƙo na jam'iyyar adawa ta ƙasa, PDP, Umar Damagum.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana haka a wani sakon da ya sanya a shafinsa na X, inda ya ƙara da cewa taron ya gudana ne a babban masallacin ƙasa dake Abuja bayan kammala sallar Juma'a.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Bayyana a Karon Farko Bayan Ya Sha Kashi Hannun Tinubu a Kotun Ƙoli

Atiku ya halarci daurin aure
Atiku ya halarci daurin aure bayan hukuncin kotun koli Hoto: @atiku. @officialABAT
Asali: Twitter

Legit Hausa ta lura cewa taron shi ne karo na farko da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP ya fita cikin jama'a bayan da kotun koli ta yi watsi da ƙarar da ya ɗaukaka kan nasarar da shugaba Bola Tinubu ya samu a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukuncin kotun ƙoli: Atiku ya yi shiru

Duk da cewa PDP ta fitar da sanarwar yin Allah wadai da hukuncin da kotun koli ta yanke, har yanzu Atiku bai mayar da martani kan lamarin ba.

Baya ga iƙirarin cewa an tafka masa magudi a zaɓen, Atiku ya kuma yi ƙoƙarin ganin an tsige Shugaba Tinubu kan zargin yin amfani da takardun bogi.

Ƙoƙarin nasa ya kasa samun sakamako mai kyau yayin da kotun koli ta amince da hukuncin kotun zaɓe, tare da tabbatar da nasarar Tinubu.

Kara karanta wannan

Abun Mamaki: Gwamnan PDP Ya Je Villa Tare da Ƙusoshin APC, Ya Taya Tinubu Murnar Nasara a Kotu

Kotun ta kuma yi watsi da ƙarar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya shigar.

Ganduje Ya Magantu Kan Atiku da Peter Obi

A wani labarin kuma, shugaban jam'iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi tsokaci kan hukuncin da kotun ƙoli ta yanke.

Ganduje ya bukaci dan takarar PDP, Atiku Abubakar da takwaransa na LP, Peter Obi da su jira zuwa 2031 domin cimma kudirinsu na son zama shugaban kasa Bayan cikar wa'adin mulkin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng