Ke Duniya: An Kama Karamin Yaron da Ya Halaka Mahaifiya Yar Shekara 58 a Gombe

Ke Duniya: An Kama Karamin Yaron da Ya Halaka Mahaifiya Yar Shekara 58 a Gombe

  • Jami'an yan sanda sun kama matashin yaro ɗan shekara 18, Adamu Isah Abbati bisa zargin halaka mata yar shekara
  • Kakakin hukumar ƴan sanda reshen jihar Gombe, ASP Mahid Mu'azu, ya bayyana yadda lamarin ya faru tun daga farko
  • Wanda ake zargin ya amsa laifinsa, ya ce ya kashe ta ne da wuƙa a cikin ɗakinta kuma ya gudu

Jihar Gombe - Rundunar ƴan sanda reshen jihar Gombe ta cafke wani matashin yaro ɗan shekara 18, Mustapha Adamu Isah, wanda aka fi sani da Abbati, bisa zargin kashe wata mata.

The Nation ta ce Ƴan sanda sun kama Abbati, wanda ake zargi da halaka Hajiya Aishatu Abdullahi wacce ake kira da Damori a Unguwar Jekadafari Quarters da ke cikin Gombe.

An kama wanda ya kashe matar aure a Gombe.
Ke Duniya: An Kama Karamin Yaron da Ya Halaka Mahaifiya Yar Shekara 58 a Gombe Hoto: thenation
Asali: UGC

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, ASP Mahid Mua’zu, shi ne ya bayyana haka yayin da yake nuna wanda ake zargin a hedkwatar ƴan sanda ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Saki Shugaban IPOB Nnamdi Kanu? Gaskiya Ta Bayyana

Ya ce ranar Jumu'a 20 ga watan Oktoba, ƴan sandan Caji Ofis ɗin Pantami suka samu korafi daga ɗan matar cewa wani makashi da bai gane ko waye ba ya yi wa mahaifiyarsa yankan rago.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Nan take jami'an Caji Ofis a Pantami suka kai ɗauki wurin, suka tarad da matar Aishatu Abdullahi, kwance cikin jini, suka ɗauke ta zuwa Asibitin koyarwa na Gombe inda aka tabbatar ta rasu."

Ta ya aka kama wanda ake zargin?

Kakakin 'yan sandan ya ƙara da cewa an kama Abbati ranar 22 ga watan Oktoba, 2023 bisa zargin hannu a kisan matar bayan samun sahihan bayanan sirri daga tawagar bincike.

A cewarsa, a yayin gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa ya shiga dakin Aishatu Abdullahi ne domin neman sufanarsa da ta kwace.

Wanda ake zargin ya kuma ambaci abokinsa, Idris Abubakar Danjauro, mai shekaru 17, wanda ya ce ya zo ɗakin ya tama shi aikata wannan ɗanyen aikin.

Kara karanta wannan

Assha: Yadda Rashin Jituwa Ta Sanya Magidanci Ya Halaka Matarsa da Wuka

Sai dai Idris, wanda aka kama daga baya, ya musanta cewa bai san wanda ya kashe matar ba a lokacin da bincike ya biyo ta kansa, Tribune ta rahoto.

Yadda lamarin ya faru tun farko

“Wanda ake zargin ya bayyana cewa Aishatu ta dawo daga makwabta, ta same shi a dakinta, ta tuhume shi tare da umartan ya fice mata daga ɗaki amma ya ki fita."
"Wanda hakan ya sa ya afka mata, ya shake ta, ya kashe ta da wuka, ya tsere ta bayan gida zuwa inda ba a sani ba."

- ASP Mahid Muazu.

Yan Bindiga Sun Kara Shiga Rukunin Gidaje

A wani rahoton daban Ƴan bindiga sun sake shiga wani rukunin gidaje a yankin Kubwa a birnin tarayya Abuja, sun sace mutane uku.

Wata majiya ta ce maharan sun kai farmakin da misalin ƙarfe 9:00 na dare, inda suka ɗauki mata da miji da wani mutum ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262