Yan Bindiga Sun Kara Shiga Rukunin Gidaje, Sun Yi Garkuwa da Mutane a Abuja

Yan Bindiga Sun Kara Shiga Rukunin Gidaje, Sun Yi Garkuwa da Mutane a Abuja

  • Ƴan bindiga sun sake shiga wani rukunin gidaje a yankin Kubwa a birnin tarayya Abuja, sun sace mutane uku
  • Wata majiya ta ce maharan sun kai farmakin da misalin ƙarfe 9:00 na dare, inda suka ɗauki mata da miji da wani mutum ɗaya
  • Ta ce 'yan banga tare da wasu tsirarun 'yan sanda sun yi ƙoƙarin korar maharan amma sun fi su yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT Abuja - Tsagerun 'yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa ne sun ɗauki mutum uku a rukunin gidajen Grow Homes da ke Kuchibiyi a yankun Kubwa cikin Abuja.

Wannan sabon harin na daren ranar Alhamis da ta wuce na zuwa ne kusan watanni takwas bayan 'yan bindiga sun shiga rukunin gudajen, sun sace mutane tara.

Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane a Abuja.
Yan Bindiga Sun Kara Shiga Rukunin Gidaje, Sun Yi Garkuwa da Mutane a Abuja Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa mutane ukun da mahara suka sace a sabon harin shekaran jiya, sun haɗa da mata da miji da wani mutum ɗaya.

Kara karanta wannan

Innnalillahi: Mutane da Dama Sun Mutu Yayin da Wani Jirgi Ya Gamu da Matsala a Jihar APC

Lokacin da wakilinmu ya ziyarci yankin da safiyar Juma’a, mazauna yankin sun firgita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa ‘yan bindigar, sun tsere ne ta hanyar wani daji, wanda ya hada yankin da lamarin ya afku da wani kauye.

Wata majiya daga cikin jami'an tsaron yankin wanda ta dage a sakaya sunanta saboda bata da hurumin yin magana da manema labarai ta ce, lamarin ya faru da ƙarfe 9:00 na dare.

Yadda sabon harin ya auku

Majiyar ta bayyana cewa daga zuwan ƴan bindigan suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi domin tsorata mazauna yankin, rahoton Guardian ya tattaro.

Da take bada labarin yadda abun ya faru, majiyar ta ce:

"Ranar Alhamis da misalin karfe 9 na dare, mu (yan banga) muka ji karar harbin bindiga. Bayan jin karar, mu da wasu jami’an ‘yan sanda na Najeriya Mobile Police (MOPOL) muka tafi gano meke faruwa."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sama da 100 Sun Sheƙa Lahira Yayin da Jirgin Sojin Sama Ya Sakar Musu Wuta a Jihohi 2

" A kan hanya muka haɗu da jami'in mu, ya faɗa mana cewa yan bindiga ne da suka kai adadin 20, sun harbe shi a hannu. Muka kara jin ƙarar harbi, suka buɗe mana wuta, muka maida martani."
"Dole muka ja da baya saboda suna da yawa, sun ɗauki mutun uku. ma'aurata mata da miji da kuma wani mutum ɗaya, har yamzu ba su tuntuɓi kowa ba."

Da aka tuntubi jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, Josephine Adeh, ta ce za ta dawo ta yi magana da yan jarida daga baya.

Jirgin ruwa ya yi haɗari a Legas

A wani rahoton na daban An rasa rayuka yayin da wani jirgin ruwa ya kife a yankin ƙauyen Isawo da ke ƙaramar hukumar Ikorodu a jihar Legas.

Mutum biyu mata ake tsammanin sun mutu sanadin kifewar jirgin ruwa yayin da wasu huɗu kuma suka jikkata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262