“Dadina Da Gobe Saurin Zuwa”: Kalaman Mawaki Rarara Sun Tayar da Kura a Tsakanin Yan Najeriya

“Dadina Da Gobe Saurin Zuwa”: Kalaman Mawaki Rarara Sun Tayar da Kura a Tsakanin Yan Najeriya

  • Kalaman mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara na ci gaba da tayar da kura a cikin kasar
  • Rarara ya fito ya soki irin salon mulkin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a kasar
  • Yan Najeriya sun yi wa mawakin caaa a kai cewa ya nuna butulci, wasu sun ce da sannu zai yi wa shugaban kasa Bola Tinubu irin haka

Kalaman da shahararren mawakin Najeriya, Dauda Kahutu Rarara ya yi a kan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, sun tayar da kura a kasar.

Yan Najeriya sun ce Rarara ya nuna butulci
“Dadina Da Gobe Saurin Zuwa”: Kalaman Mawaki Rarara Sun Tayar da Kura a Tsakanin Yan Najeriya Hoto: Muhammadu Buhari, Dauda Rarara.
Asali: Facebook

Abun da Rarara ya fadi kan Buhari

Rarara wanda ya kasance mawakin Buhari ya caccaki irin salon mulkin tsohon shugaban kasar inda ya ce sai da ya kashe kasar gaba daya sannan ya mika mulki ga magajinsa, Shugaban kasa Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Jiga-jigan PDP 4 da Su ka Nuna Farin Ciki da Nasarar Tinubu Kan Atiku a Kotun Koli

Harma mawakin ya bayyana a cikin wani faifan bidiyo cewa ya yi danasanin goyon bayan tsohon shugaban kasar da ya yi, domin a cewarsa ya kyautata masa zato amma sai aka samu akasin haka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abun da yan Najeriya ke fadi kan kalaman Rarara

Wannan kalamai nasa sun sa kasar ta dauki dumi inda mutane da dama musamman a soshiyal midiya suka dunga bayyana ra'ayoyinsu.

Yan Najeriya da dama sun caccaki mawakin inda wasu suka kira shi da butulu, wasu kuma sun ce sun san za a rina domin dai munafurci dodo ne.

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin mabiyanta na Facebook a kasa:

Abdullahi Adamu ya yi martani:

"Rarara ya tabbatar wa Duniya chewa shi butuli ne Gobe akan Tinubu zaiyi magana."

Auwal Nuhu Idrees ya ce:

"Shifa wannan mawakin sha shane."

Kara karanta wannan

Rarara: Tsohon Hadimi Ya Mayar Wa Mawaki Raddi Mai Zafi Saboda Caccakar Mulkin Buhari

Muhammad Shuaibu ya yi martani:

"Kafadi gaskiya dama kuma mutane basasanta."

Malam Tirmizi Salisu Gude ya ce:

"Masha Allah.
"Dadina DA gobe saurin zuwa."

Muhammad Haruna Tsoho ya yi martani:

"Allah Mai iko dadina da gobe saurin zuwa tun aduniya ma kenn anfara dibar ta zuci kan aje wajen Allah."

Isah Skalit Once ta ce:

"MUNAFINCI DODO NE.
"Da Rara Yayiwa Buhari Abinda,Buhari yayiwa ‘Yan Najeriya. Masha Allah."

Abba Umar Ado ya ce:

"Alhamdulillah Alhakin talaka wasane tun a duniya Kennan ."

"Na cancanci kujerar minista" - Rarara

A gefe guda, Dauda Adamu Kahutu ‘Rarara’ ya kira taron manema labarai, a nan ya tofa albarkacin bakinsa a game da mulkin Bola Ahmed Tinubu.

Rarara ya bayyana cewa ya bada gudumuwa sosai wajen kafuwar gwamnatocin APC yayin da ake taya Bola Tinubu murnar samun nasara a kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng