Emefiele Ya Sake Fadawa Matsala Bayan EFCC Ta Cafke Shi Yayin da Ya Shaki Iskar Yanci
- Tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele na tsare a hukumar EFCC don amsa wasu tambayoyi kan sabbin zarge-zarge
- Wannan na zuwa ne awanni kadan bayan Hukumar DSS ta sako tsohon gwamnan a jiya Alhamis 26 ga watan Oktoba a Abuja
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa Emefiele na amsa tambayoyi a hedikwatar hukumar da ke Jabi Abuja kan badakalar kudade
FCT, Abuja – Hukumar Yaki da Cin Hanci, EFCC ta garkame tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Punch ta tattaro cewa Emefiele na amsa tambayoyi a ofishin hukumar da ke birnin Abuja bayan sun kama shi a daren jiya Alhamis 26 ga watan Oktoba, Legit ta tattaro.
Yaushe hukumar EFFC ta kama Emefiele a Abuja?
Wannan na zuwa ne awanni kadan bayan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, DSS ta sako Emefiele daga kulle yayin da ake ci gaba da bincikarshi.
Gwamnan APC Ya Gana da Babban Hafsan Tsaro, Ya Faɗi Dalili Ɗaya Tak da Zai Sa Ya Tattauna da 'Yan Bindiga
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya daga hukumar EFFC ta tabbatar a yau Juma'a 27 ga watan Oktoba cewa tsohon gwamnan na ofishinsu ya na amsa tambayoyi.
Majiyar ta ce:
“Tabbas Emefiele yanzu haka ya na tare da mu.
“Ya na amsa tambayoyi a hedikwatar hukumar da ke Abuja kan zargin badakalar makudan kudade da sauran abubuwa yayin da ya ke shugabancin bankin.”
Wane hali Emefiele ya saka 'yan Najeriya?
'Yan Najeriya da dama a baya sun caccaki tsarin da tsohon gwamnan bankin ya kawo wadanda su ka jefa al'umma cikin matsin tattalin arziki, cewar PM News.
Daga cikin sabbin tsare-tsaren da Emefiele ya kawo sun hada da sauya fasalin naira da takaita yawan cire kudade a asusun bankunan mutane.
Wadannan matakai sun jefa 'yan kasar cikin mummunan yanayi inda ake tunanin an yi su ne don kawo cikas a cin zaben Shugaba Tinubu.
Bidiyo: DSS ta saki tsohon shugaban EFCC, Bawa
A wani labarin, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, DSS ta saki tsohon shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa bayan shafe kwanaki 134 a tsare.
Bawa ya shiga hannun hukumar ta DSS a ranar 14 ga watan Yuni jim kadan bayan Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi a mukaminsa.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari shi ya nada Bawa mukamin shugaban hukumar don dakile cin hanci da rashawa a kasar.
Asali: Legit.ng