Sojoji Sun Sheke Kasurguman 'Yan Boko Haram 6, Sun Kuma Cafke Ma Su Taimakon 'Yan Bindiga
- Rundunar sojin Najeriya ta sheke mayakan Boko Haram guda shida a karamar hukumar Geidam da ke jihar Yobe
- Mataimakin daraktan yada labarai na rundunar Kyaftin Muhammad Shehu shi ya bayyana haka a jiya Alhamis 26 ga watan Oktoba
- Ya ce rundunar ta samu nasarar ce bayan samun bayanan sirri daga jama'a a kauyen Jororo da ke jihar
Jihar Yobe - Rundunar sojin bataliya ta 159 ta yi ajalin mayakan Boko Haram guda 6 tare da muggan makamai a jihar Yobe.
Mataimakin daraktan yada labarai na sashi na 2, Kyaftin Muhammad Shehu shi ya bayyana haka a ranar Alhamis 26 ga watan Oktoba.
Wace nasara rundunar sojin ta samu kan Boko Haram?
Shehu ya ce rundunar ta samu nasarar ce a kauyen Jororo a karamar hukumar Geidam da ke jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce nasarar ta samu ne bayan samun bayanan sirri daga mutanen gari, cewar Daily Trust.
Ya kara da cewa yayin arangamar, sojoji sun hallaka mayakan biyu tare da kwato babura da wayoyin salula.
A daya bangaren, Shehu ya ce an hallaka mayakan hudu a jiya Alhamis a Babbangida a karamar hukumar Tarmuwa da ke jihar.
Ya ce wannan na zuwa ne bayan samun bayanan sirrin cewa akwai 'yan Boko Haram a kauyukan Bajingo da Kurnawa.
An kama ma su taimakon 'yan bindiga
Har ila yau, a jihar Kaduna, rundunar ta kama masu safarar makamai ga 'yan bindigan a karamar hukumar Kachia da ke jihar.
Kanal Musa Yahaya, mataimakin daraktan hulda da jama'a na rundunar shi ya bayyana haka inda ya ce sun samu bayanan sirri a ranar Talata 24 ga watan Oktoba.
Ya bayyana sunayensu da Shuaibu Lawan da kuma Salihu Usman wanda aka samu muggan makamai a tare da su da kuma babura.
'Yan Boko Haram sun hallaka mutane 4 a Borno
A wani labarin, mayakan Boka Haram sun yi wa wasu mutane kwanton bauna tare da hallaka su a jihar Borno.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin 25 ga watan Satumba a kan hanyar Gwoza Limankara da ke da nisan kilomita 134 daga Maiduguri.
Arewa maso Gabas na fama da hare-haren mayakan Boko Haram musamman a kauyukan jihohin Borno da Yobe da ke yankin.
Asali: Legit.ng