Sarkin Ogbomosho da Kotu Ta Tsige Zai Daukaka Kara

Sarkin Ogbomosho da Kotu Ta Tsige Zai Daukaka Kara

  • An samu hatsaniya a kan sarautar Soun na Ogbomosho bayan rasuwar Oba Ajagungbade III a watan Disamba 2021
  • Wata babbar kotu a jihar Oyo ta kori Oba Ghandi Afolabi Olaoye a ranar Laraba, 25 ga watan Oktoba, wanda aka naɗa a matsayin sabon Soun na Ogbomosho
  • Sai dai, sansanin sabon sarkin ya yi martani kan hukuncin kotun tare da shan alwashin daukaka ƙara domin neman adalci

Ogbomosho, jihar Oyo - Sansanin Oba Ghandi Afolabi Olaoye, Soun na Ogbomosho wanda wata babbar kotun jihar Oyo ta kora, ya bayyana cewa sarkin zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

Idan dai za a iya tunawa, a makonnin da suka gabata ne masu zaɓar sarki suka zaɓi Olaoye, wanda fasto ne kuma ɗan kasuwa mai kasuwanci a ƙasashen waje a matsayin sabon Sarkin Ogbomosho wanda ake kira da Soun.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Sahihancin Nasarar Aminu Tambuwal a Matsayin Sanata PDP

Sarkin Ogbomosho zai daukaka kara
Sarkin Ogbomosho zai daukaka kara kan hukuncin kotu na tsige shi Hoto: @Yorubaness, @Agegeborn
Asali: Twitter

Sai dai, kuma Yarima Kabir Mohammed Olaoye yana ƙalubalantar wannan hukuncin na masu zaɓar sarkin.

Ogbomosho: Soun zai ɗaukaka ƙara, majiyar fada

A ranar Laraba, 25 ga watan Oktoba, kotun ta soke zaɓe da kuma naɗin da aka yi masa a matsayin Soun na Ogbomosho.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alƙalin kotun, mai shari'a K.A. Adedokun, ya tsige sabon sarkin daga kan karagar mulki a yayin da yake zartar da hukunci kan ƙarar da Yarima Kabir ya shigar.

Da yake zantawa da jaridar The Punch dangane da faruwar lamarin, wani majiyar fadar ya bayyana cewa za a ɗaukaka ƙara kan hukuncin da babbar kotun ta yanke.

Domin haka ya buƙaci al'ummar garin da su kwantar da hankalinsu. Jaridar a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba ta ambato majiyar na cewa:

"Tabbas za a ɗaukaka ƙara domin haka kada mutane su damu. A shari’ar da Yarima Olaoye ya shigar, alƙalin ya ce an bi tsarin da ya dace, amma yanzu kuma an ce ba a bi tsarin da ya dace ba. Abun akwai ruɗani, kotun ɗaukaka ƙara za ta warware hakan. Jama'a su kwantar da hankukansu."

Kara karanta wannan

Babbar Kotu Ta Tsige Fitaccen Sarki Mai Daraja a Najeriya, Ta Bada Sabon Umarni

Basarake da Aka Kora a Katsina Ya Yi Martani

A wani labarin kuma, tuɓaɓɓen hakimin Kuraye a ƙaramar hukumar Charanchi ta jihar Katsina ya yi martani kan sauke shi daga sarauta da gwamnatin jihar Katsina ta yi.

Alhaji Abubakar Abdullahi Ahmadu ya kare kansa daga zargin da aka yi masa na cewa ya ɗaura aure ba tare da bincike ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng