Nasarawa: Malamar Jami'ar da 'Yan Bindiga Suka Sace Ta Samu 'Yanci

Nasarawa: Malamar Jami'ar da 'Yan Bindiga Suka Sace Ta Samu 'Yanci

  • Malamar jami'ar jihar Nasarawa da ke Keffi, Dakta Comfort Adokwe da ƴan bindiga suka sace ta samu ƴanci
  • Dakta Comfort ta samu ƴanci ne daga sace da ƴan bindiga suka yi bayan an biya maƙudan kuɗin fansa har N5m
  • Majiyoyi sun tabbatar da sakin malamar jami'ar wacce yanzu hake ke kwance a asibiti domin duba lafiyarta sakamakon halin da ta shiga a hannun ƴan bindiga

Jihar Nasarawa - Malamar jami'ar jihar Nasarawa dake Keffi, Dakta Comfort Adokwe, da ƴan bindiga suka sace ta samu ƴanci.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa an sako ta ne bayan da iyalanta suka biya kuɗin fansa Naira miliyan 5 ga waɗanda suka sace ta.

An sako malamar jami'ar da aka sace
Malamar jami'ar da aka sace a Nasarawa ta samu yanci Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Ɗaya daga cikin ƴan uwanta, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta tabbatarwa da jaridar Punch sakin malamar jami'ar.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Wasu Hatsabiban 'Yan Fashi Biyu Suka Tsere Daga Gidan Yari a Jihar Arewa

Sai dai majiyar ta ce sakamakon halin da ta shiga a hannun ƴan bindigan, yanzu haka tana asibiti domin a duba lafiyarta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A daren ranar Lahadi, 22 ga watan Oktoba, wasu ƴan bindiga suka yi awon gaba da Dakta Adokwe, a gidanta da ke Angwan Jaba a garin Keffi.

Rahotanni sun ce maharan sun kutsa kai cikin gidanta inda suka yi ta harbe-harbe a iska kafin daga bisani su tasa ƙeyarta.

Yaushe aka sako malamar jami'ar?

Wani ɗan uwan malamar, Mista Timothy Adokwe, ya bayyana cewa, an sako malamar ne daga hannun waɗanda suka sace ta da misalin ƙarfe 10:00 na daren ranar Talata bayan an biya maƙudan kuɗin fansa.

A cewarsa, jami’an tsaro sun yi iyakacin ƙoƙarinsu wajen bin diddigin waɗanda suka yi garkuwa da ita, amma an dakatar da su daga ɗaukar duk wasu tsauraran matakan da za su jefa rayuwar malamar cikin haɗari.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Malamar Jami'a a Wani Sabon Hari a Arewacin Najeriya

A kalamansa:

"Mun fi son mu ga mun ceto ƴar uwarmu. Jami’an tsaro sun yi iya ƙoƙarinsu, sun taimaka wajen gano inda suke."
"Amma bisa gargaɗin da waɗanda suka sace ta suka yi cewa za su kashe ta idan wani abu ya faru, mun roƙi jami'an tsaro da ka da su yi wani abu da zai kawo cikas ga rayuwarta."
"Na san cewa jami'an tsaro sun sa ido kan komai kuma suna iya bin ƴan ta'addan."

'Yan Bindiga da Dama Sun Halaka

A wani labarin kuma, ƴan bindiga da dama sun rasa rayukansu bayan sun kawo harin ramuwar gayya a ƙauyen Tukandu na jihar Kebbi.

Ƴan bindigan waɗanda suka zo ɗaukar fansar kisan da aka yi wa wani ɗan bindiga, sun gamu da ajalinsu ne a hannun jami'an tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng