“Ku Zo Da Barkono”: Budurwa Ta Lissafa Abubuwan Da Ya Kamata Masu Shirin Komawa Kanada Su Riko

“Ku Zo Da Barkono”: Budurwa Ta Lissafa Abubuwan Da Ya Kamata Masu Shirin Komawa Kanada Su Riko

  • Wata matashiyar budurwa yar Najeriya da ke zaune a Kanada ta shawarci matafiya da su riko wasu muhimman kayayyaki idan za su zo
  • Matashiyar, Temmy, ta dage cewa riko garin kwaki, taliya, barkono, soso da sauran kayayyaki zai taimakawa dalibai masu shirin komawa Kanada
  • Wasu yan Najeriya da ke kasar sun yarda da shawararta sannan sun ce suma sun tafi da wasu kayayyakin abinci na gida

Wata budurwa yar Najeriya da ke zaune a Kanada ta bayar da wasu yan shawarwari kan muhimman abubuwan da ya kamata matafiya su zo da su kasar.

Matashiyar, Temmy, ta yi bidiyo sannan ta wallafa a TikTok don taimakawa yan Najeriya masu shirin zuwa kasar domin su gane abubuwan da ya kamata su riko.

Matashiya ta shawarci mutane kan abun da za su riko zuwa Turai
“Ku Zo Da Barkono”: Budurwa Ta Lissafa Abubuwan Da Ya Kamata Masu Shirin Komawa Kanada Su Riko Hoto: TikTok/@igobytemmy
Asali: TikTok

A bidiyon, Temmy ta bayyana cewa kawo abubuwa kamar su audugar mata, barkono, soson wanka, da tafiya zai taimaka sosai.

Kara karanta wannan

Hanya 1 Za a Bi Domin Hana Farashin Dala Tashi - Tsohon Mataimakin Sanusi a CBN

Ta ce sauran abubuwan da za ta shawarci mutane su riko zuwa Kanada sun hada garin kwaki, kayan abinci, madara, na'urar adafta, da kuma gashi yan kanti.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kan bukatar riko na'urar adafta, Temmy ta ce:

"Ba zan iya daina jaddada wannan ba. Kuna bukatar wannan don hana hauhawar kudin wuta na kayan lantarki da ma cajar waya da aka saya a wajen kasar da za ku."

Masu amfani da TikTok sun yi martani

@Nofi ta ce:

"A'a! Saboda ba zan iya rayuwa ba tare da Always ba."

@Saltandpepper ta ce:

"Na ji wai ba a barin madara."

@Boyfromspace ya ce:

"Kayan abinci ne ya kamata ya fara zuwa a farko saboda me zai hana?"

@Anyanwu ututu ta yi martani:

"Kenan babu wanda ke son tunawa da ka tanadi gyada saboda garin kwakin."

@prvncedafirst ya yi martani:

Kara karanta wannan

Jerin Manyan 'Yan Takara 5 da Jam'iyyun da Za Su Fafata a Zaben Jihar Kogi a Wata Mai Kamawa

"Ya batun maza fa? Me za mu riko?"

Matashi ya gina gida 3 da sana'ar kosai

A wani labari na daban, mun ji cewa wani mutum mai suna Chibueze Damian, wanda ya fito daga kabilar Ibo da ke sana'ar soya kosai ya yadu a soshiyal midiya.

Da aka yi hira da shi, mutumin ya bayyana cewa ya fara siyar da kosai tun 1998 kuma ya shafe fiye da shekaru 20 a kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng