Za Mu Sa Kafar Wando Daya Inji Nyesom Wike da Ya Shirya Yaki da Manya a Abuja

Za Mu Sa Kafar Wando Daya Inji Nyesom Wike da Ya Shirya Yaki da Manya a Abuja

  • Ezenwo Nyesom Wike ya shaida cewa da gaske yake yi wajen maganar tara kudin haraji bayan nada shi a matsayin Minista
  • Babban Ministan harkokin birnin tarayyan na Abuja ya shaidawa shugaban kungiyar NUJ cewa zai yi yaki a kan harajin filaye
  • Wike ya gargadi wadanda su ka mallaki filaye a birnin Abuja su biya gwamnati hakkinta, idan ba haka ba za a karbe kadarorinsu

Abuja- A matsayinsa na Ministan harkokin birnin tarayya, Ezenwo Nyesom Wike, ya ja-kunnen wadanda ba su biyan harajin filayensu.

Vanguard ta ce Mista Ezenwo Nyesom Wike ya bukaci wadanda ake bi bashi su sauke nauyin da yake kan su kafin wa’adin da ya bada.

Idan lokacin afuwar da aka yanke ya wuce, Nyesom Wike ya ce za a ga aiki da cikawa kwanaki bayan ya farfado da dokokin haraji.

Kara karanta wannan

“Wike Na Da Laifinsa”: MURIC Ta Goyi Bayan Gumi Yayin Da Ya Kira Ministan Abuja ‘Shaidani’

Nyesom Wike
Nyesom Wike a ofishinsa a Abuja Hoto: @Topboychriss
Asali: Twitter

Nyesom Wike zai karbe filaye a kan haraji

Alwashin da Ministan ya sha shi ne zai karbe filayen da ba a biya masu haraji, ya jaddada haka da ya zauna da shugaban kungiyar NUJ.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya shaidawa Chris Isiguzo a wajen wani taro a Abuja cewa ba cika-baki kurum ya ke yi ba, zai aikata duk abin da ya yi alkawari.

A karshen wa’adin da ya bada, an rahoto Ministan na birnin tarayya ya na cewa ‘wani abu zai faru’.

Babu maganar watsi da kwangila a Abuja

Tsohon Gwamnan jihar Ribas ya kuma shaidawa kungiyar ‘yan jaridan cewa an zo karshen lokacin da za a bada kwangila, ayi watsi da ita.

"Idan ana maganar watsi da kwangila a birnin tarayya, ya zo karshe. Wannan ba zai yiwu sai saboda shugaban kasa ya cire mu daga TSA.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari Ya Yi Ya Jawo darajar Naira ta ke Karyewa a Yau – Sanatan PDP

Yanzu da na ke magana da ku, zan iya fada maku nawa mu ka samu daga kudin shiga. Za a cigaba da sakin kudin kwangilolin FCTA.
Wasu su na cewa abin da mu ke yi hargowar banza ce kurum, amma ina so in sanar da su cewa a karshen lamarin, wani abin zai faru.
Za mu taka wasu, ba za ka iya yin shugabanci ba tare da taka wasu ba. Ba ni na yi doka ba, amma ni da abokiyar aiki na za mu dabbaka su."

- Ezenwo Nyesom Wike

Shari'ar zaben Shugaban kasa

Kotun koli a ranar Laraba, ta sanar da cewa Bola Tinubu, Atiku Abubakar da kuma Peter Obi za su san makomarsu a shari’ar zabe nan da sa'a 24.

Idan ‘yan adawa sun yi nasara, Bola Tinubu zai iya rasa mulki, idan akasin haka ta faru, za a jira 2027 da za a sake kada gangar takara a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng