Miyagun 'Yan Bindiga Sun Halaka 'Yan Gudun Hijira Uku a Jihar Benuwai
- Tsagerun 'yan bindiga sun tare 'yan gudun hijira, sun harbe su har lahira a jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiya
- Rahotanni sun bayyana cewa mutanen uku da aka kashe sun tafi kamun kifi, ba zato 'yan ta'addan suka tare su kuma suka kashe su
- Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda reshen jihar, SP Anene, ta ce har yanzun rahoton faruwar lamarin bai iso gare su ba
Jihar Benue - Rahotanni sun nuna cewa wasu ƴan bindiga sun halaka ƴan gudun hijira uku, waɗanda suka tafi kamun kifi a ƙaramar hukumar Gwer ta yamma a jihar Benuwai.
Shugaban sansanin 'yan gudun hijira na ƙaramar hukumar Gwer ta yamma, Ibaah Terna Jacob, ne ya tabbatar da haka ga wakilin jaridar Daily Trust.
Mutanen sun je kamun kifi ne a ranar Litinin din da ta gabata amma maharan dauke da makamai suka tare su, kana suka harbe su har lahira.
Ya kuma bayyana sunayen waɗan da 'yan bindigan suka kashe, sun haɗa da, Igbahemba Abua, Iorhemba Cletus da kuma Akaa Clifford.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda lamarin ya faru
Jacob ya ce mutanen uku sun tafi kamun kifi a gundumar Gbange/Tongov da ke ƙaramar hukumar Gwer ta yamma kuma ba su dawo ba har dare ya yi.
A cewarsa, yayin da aka tafi nemansu ne wani da ya shaida lamarin ya faɗa musu cewa wasu mahara dauke da makamai ne suka bi su kana suka bude musu wuta.
Shugaban sansanin ƴan gudun hijiran ya kuma ƙara da cewa bayan tsananta bincike, an samu nasarar gano gawarwakin mutanen guda uku da safiyar ranar Talata.
Sai dai a jawabinsa, Mista Jacob ya ce bayan gano gawarsu, ba a yi wani dogon jinkiri ba aka binne su, kamar yadda The Sun ta ruwaito.
Amma yayin da aka tuntuɓi jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sanda reshen jihar Benuwai, SP Catherine Anene, ta ce har yanzu rahoto bai ƙariso kan teburinta ba.
'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Masallaci
A wani labarin kuma Yan bindiga sun kai hari Masallaci lokacin sallar asuba a ƙauyen Sabon Layi, ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.
Bayanai sun nuna cewa maharan sun kashe limamin Masallacin tare da wani mutum ɗaya yayin da wasu masallata biyu suka ji raunuka.
Asali: Legit.ng