Ogun: Kwastoma Ya Yi Yunkurin Kona Banki Bayan An Wawushe Masa Kudade

Ogun: Kwastoma Ya Yi Yunkurin Kona Banki Bayan An Wawushe Masa Kudade

  • Wani fusataccen kwastoma ya yanke shawarar ƙona bankin GT Bank a jihar Ogun bayan kudaɗensa sun yi ɓatan dabo
  • Kwastoman dai ya yi hakan ne bayan N500,000 ta ɓace sama ko ƙasa daga asusunsa na a jiya a bankin
  • Sai dai, an yi nasarar dakarar da shi inda aka miƙa shi hannun ƴan sanda domin ɗaukar matakin da ya dace

Jihar Ogun - An kama wani mutum mai suna Sodirudeen Rufa'i bisa yunƙurin bankawa ginin bankin GT Bank da ke unguwar Oke-Ilewo, ranar Talata a birnin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Wanda ake zargin ya yi iƙirarin cewa ya yanke hukuncin ƙona bankin ne bayan bankin ya ƙi yin komai kan ƙorafe-ƙorafen da ya yi na cewa an cire masa N500,000 ba tare da izini ba daga asusunsa, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Mata Mai Shayarwa da Wasu Mutane Masu Yawa a Jihar Arewa

Kwastoma ya yi yunkurin kona banki a Ogun
Kwastoma ya yi yunkurin cinnawa banki wuta a Ogun Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Twitter

Lokacin da ya kai lamarin a gaban hukumomi, sun ba shi shawarar ya jira bankin ya bi hanyar da ta dace domin gano abin da ya faru da kuɗaɗensa.

Lamarin ya ƙara muni ne lokacin da bankin ya sanar da shi zambar kuɗaɗensa aka yi masa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwastoma ya yi yunƙurin ƙona banki

Bayan samun labarin hakan daga wajen jami’in bankin, sai kawai Rufa’i ya koma bankin ɗauke da man fetur inda ya fara watsawa a harabar bankin, rahoton Gistlover ya tabbatar.

A yayin da hakan ke faruwa, wasu daga cikin kwastomomin da ke cikin bankin sun yi ƙoƙarin tsira da ransu, yayin da wasu tare da jami'an tsaron bankin suka ƙwace abin kyastawar da ke hannunsa kafin ya kai ga amfani da ita.

Babban jami'in tsaro na bankin, Godwin James, ya miƙa wanda ake zargin zuwa ofishin ƴan sanda na Ibara.

Kara karanta wannan

Assha: Yadda Rashin Jituwa Ta Sanya Magidanci Ya Halaka Matarsa da Wuka

Meyasa ya yi yunƙurin ƙona bankin?

A halin da ake ciki, yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya yi iƙirarin cewa ya ɗauki matakin ne domin jan hankalin hukumomin da suka dace game da abin da bankin ya yi da kuɗaɗensa.

Jami'in hulɗa da jamava na rundunar ƴan sandan jihar, Omolola Odutola, ya ce za a tuhumi Rufa’i da yunƙurin kashe kansa da kuma kisan kai.

Kwastoma Ya Mutu a Banki

A baya rahoto ya zo kan yadda wani kwastoma ya yanke jiki ya faɗi a cikin harabar wani banki a jihar Delta.

Mutumin dai ya yanke jiki ya faɗi ne bayan ya kwashe tsawon sa'o'i yana jiran layi ya zo kansa domin ya cire kuɗi a ATM.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng